Subscribe Our Channel

TA YAYA ZA A CE: ALLAH YANA KO'INA ALHALI KOWA ZUCIYARSA DA FITIRARSA SUNA JIN CEWA: ALLAH YA DAUKAKA A SAMAN KOMAI GABA DAYA?!

Abul Hassan Al- Ash'ariy (r) ya ce:
رأينا المسلمين جميعا يرفعون أيديهم إذا دعوا نحو السماء؛ لأن الله تعالى مستو على العرش الذي هو فوق السماوات، فلولا أن الله عز وجل على العرش لم يرفعوا أيديهم نحو العرش، كما لا يحطّونها إذا دعوا إلى الأرض
الإبانة عن أصول الديانة (ص: 107)

"Mun ga Musulmai gaba dayansu SUNA DAGA HANAYENSU ZUWA SAMA IDAN ZA SU YI ADDU'A, SABODA SUNA JIN CEWA: ALLAH YA DAUKAKA A KAN AL'ARSHI WANDA YAKE SAMAN SAMMAI, BA DON ALLAH YANA SAMAN AL'ARSHI BA DA BA SU DAGA HANAYENSU SETIN AL'ARSHIN BA, KAMAR YADDA BA SA SAUKE HANAYEN NASU KASA IDAN ZA SU YI ADDU'A".

1- Mai wannar magana shi ne: ABUL HASSAN AL'ASH'ARIY, LIMAMIN MAZHABAR ASH'ARIYYA, ga shi shi da kansa yana kafa hujja da FITIRA wajen tabbatar da cewa: Allah yana sama, ya daukaka a kan Al'arshinsa.
2- In ka ce: Allah yana ko'ina, ya shiga cikin komai, HAR WASU SUKE CEWA: KOMAI ALLAH NE, DON ME YA SA IN ZA KA YI ADDU'A KAKE DAGA HANUNKA SAMA?
DON ME YA SA BA ZA KA MIKA HANUN NAKA KASA BA, TUN DA YANA KO'INA?!
3- Fitira da take cikin jikin mutum ta tabbatar da cewa: ALLAH YANA SAMA, SHI YA SA DAGA AN CE: ALLAH, SAI MUTUM YA JI ZUCIYARSA TA NUFI SAMA, BA ZA TA NUFI DAMA KO HAGU BA, BALLE KUMA KASA.
4- Aqidar cewa: Allah yana ko'ina, Aqida ce da ta saba wa Qur'ani da Sunna da Ijma'in Musulmai da Dalilai na hankali da na Fitira.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter