ZARGIN CEWA: ANA SUKAN SHAIKH RABEE'I AL- MADKHALIY
Ni a fahimtata sau da yawa masu ta'assubanci wa Shaikh Rabee'i suna zaluntar mutane bayan sun zalunci kawunansu.
Duk da cewa; ban bibiyi farkon abin sosai ba, amma na ga wasu da suka fara fitowa suna sukan wasu Malamai guda biyu, wato Shaikh Abu Ishaq Al- Huwainiy, da Shaikh Muhammad Hassan na Masar, da sunan malamansu su Shaikh Rabee'i sun bidi'antar da su ko sun jarraha su. To bidi'antarwar su Shaikh Rabee'i gare su Ijtihadi ne ba nassi na Qur'ani ko Sunna ko Ijma'i ba, balle a ce: saba masa a kan haka Inhirafi ne, bata ne, halaka ne, bidi'a ne.
To su kuma wadanda suke daukar su Shaikh Abu Ishaq Al- Huwainiy, da Shaikh Muhammad Hassan a matsayin malaman Sunna, in sun zo sun yi martani ma wadancan, sai su ce: ai Shaikh Rabbe'i shi ne "Hamilu Liwa'il Jarhi wat Ta'adeel", don haka babu wanda ya isa ya saba masa, saba masa suka ne ga Shaikh Rabee'i, don haka duk wanda ya saba masa to ya soke shi, kuma ya zama Munharifi Dan Bidi'a, wanda ya saba hanyar Muminai.
To kun ga fa yadda ake fara da'awar ana sukan Shaikh Rabee'i din!
Su a wajensu abin da suke fada a kan su Shaikh Abu Ishaq Al- Huwainiy ba suka ba ne, bal ma Jihadi ne, sai abin da aka fada a kan Shaikh Rabee'i ne yake suka da Inhirafi, da fita daga tafarkin Muminai!!
Shin maganar Shaikh Albaniy ta "Hamilu Liwa'il Jarhi...", nassin Qur'ani ce ko Hadisi, da za ana lazimta wa mutane bin Ijtihadin Shaikh Rabee'i a Jarhinsa da yake yi wa mutane?!
Saboda haka, duk wata magana da za a gina zargin sukan Shaikh Rabee'i a kanta, da farko tana bukatar sai an tabbatar da sukan tukuna, in ya tabbata suka ne a Shari'ance sai a zargi wanda ya soke shi, don bai halasta ka soki duk wani Musulmi ba tare da hujja ta Shari'a ba. In kuma saba wa Shaikh Rabee'i a bisa Ijtihadinsa na Jarhi Inhirafi ne, to za a mayar da mu baya kenan, wato a mayar da mu ta'assubanci da bautar shehunnai. Saboda sai bin Shaikh Rabee'i ya zama wajibi kafin saba masa ya zama laifi ko suka ko inhirafi, har a sanya shi abin jarabawa wa mutane.
Mafi girman wanda Shaikh Rabee'i ya jarraha bisa hujja shi ne Sayyid Qutub, amma duk da haka akwai manyan Malamai da suka saba masa, irin su Shaikh Albaniy da Mufty Alus Shaikh da Shaikh Bakar Abu Zaid da Ibnu Jibreen da sauransu, amma a hakan masu ta'assubanci wa Shaikh Rabee'i suka mayar da Sayyid Qutub a matsayin abin jarabawa wa mutane, duk wanda ya yi magana mai kyau a kansa ya zama Dan Bidi'a. To yaya za ka yi da su Mufty Alus Shaikh kuma?!
Saboda haka, kuskure ne a zo ana juya magana daga asalin yadda take, masu ta'assubanci wa Shaikh Rabee'i su suke fara sukan malaman da wasu suke girmamawa ba tare da dalili bayyananne ba, sai kuma in an yi musu martani sai su dawo su ce ana sukan Shaikh Rabbe'i, sai su cika Facebook da posting na yabon Shaikh Rabee'i da raya cewa; ana sukansa!
A takaice; ina ba mu shawara gaba daya da cewa; bin Shaikh Rabee'i ko wani malami daban a kan Ijtihadinsa ba wajibi ba ne, don haka bai halasta a kafa shi a matsayin abin jarabawa wa mutane ba, in kuwa aka yi haka to ko shakka babu wannan ta'assubanci ne da kungiyanci abin zargi.
Haka kuma su ma sauran malamai da Shaikh Rabee'i yake yin magana a kansu ta yiwu ya tabbata suna da kurakurai, a cikinsu wanda girman kuskurensa ya kai ga fita daga Sunna to za a iya fitar da shi daga Sunna, amma bayan an tsayar masa da hujja, saboda fitar da mutane daga Sunna yana da wahala kamar yadda Imamu Ahmad ya fada.
Haka kuma su ma sauran malamai da Shaikh Rabee'i yake yin magana a kansu ta yiwu ya tabbata suna da kurakurai, a cikinsu wanda girman kuskurensa ya kai ga fita daga Sunna to za a iya fitar da shi daga Sunna, amma bayan an tsayar masa da hujja, saboda fitar da mutane daga Sunna yana da wahala kamar yadda Imamu Ahmad ya fada.
Daga karshe, ya kamata mu sani, fitar da mutane daga Sunna ba abu ne mai sauki ba, haka ba kowane kuskure ne yake fitar da mutum daga Sunna ba, babin bidi'antarwa babi ne da yake bukatar ilimi da hikima, ba jahilci da atifa ba balle kuma son rai.
Sa'annan kuma ba kowane Dan Bidi'a ne yake halakakke, ko mai sabo ba. Mutum zai iya fadawa bidi'a amma kuma yana da uzurin da zai sa ya tsira a wajen Allah, imma saboda jahilci ko tawili. Saboda haka ba za a zarge shi ko a soke shi ba, balle kuma ayi masa Uquba.
Sa'annan kuma ba kowane Dan Bidi'a ne yake halakakke, ko mai sabo ba. Mutum zai iya fadawa bidi'a amma kuma yana da uzurin da zai sa ya tsira a wajen Allah, imma saboda jahilci ko tawili. Saboda haka ba za a zarge shi ko a soke shi ba, balle kuma ayi masa Uquba.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce:
ليس كل مخطئ ولا مبتدع ولا جاهل ولا ضال يكون كافرا؛ بل ولا فاسقا بل ولا عاصيا
مجموع الفتاوى (12/ 180)
ليس كل مخطئ ولا مبتدع ولا جاهل ولا ضال يكون كافرا؛ بل ولا فاسقا بل ولا عاصيا
مجموع الفتاوى (12/ 180)
Saboda haka Dalibai mu bi a hankali, babu abin da yake haifar da rarrabuwar kan Ahlus Sunna da fitina a tsakaninsu kamar hukunci a kan mutane da bidi'antarwa ba tare da ilimi da hikima ba, abin da yake haifar da wannan kuwa shi ne ta'assubanci ma wasu malamai ban da sauran malaman, da mayar da su masu hukunci a kan mutane, kamar yadda aka mayar da Shaikh Rabee'i a matsayin mai hukunci a kan mutane, da daukan Ijtihadodinsa a matsayin abin da ya wajiba kowa ya bi.
Allah ya shiryar da mu gaba daya.
* Asalin wannan rubutu comment ne da aka yi a post din Malam Adam Sani Adam Abu-Umayrah da na Malam Adam Muhammad.