Subscribe Our Channel



YADDA 'YAN HAKIKA SUKA FICE DAGA DARIKAR TIJJANIYYA
1. Bayan shafe tsawon lokaci maluman mu na fito da tarin munanan Akidu wadanda akace an zakulo daga litattafan 'yan Tijjaniyya da kuma maganganu na sauti daga maluman su to amman sai fatawar ta sauya domin kuwa a yanzu dai akwai malumanmu da suka tabbatar cewa Yan Hakika ba Yan Tijjaniyya bane.
2. Akwai 'Yan Tijjaniyya da muka sani da yawa wadanda basa tare da yan Hakika kuma har dasu ma ana fitowa a yaki Akidar shin meye matsayin wadannan tsakanin su da 'yan hakika su waye 'yan Tijjaniyya?
3. Idan har abinda maluman mu suka fada da farko gaskiyane ta tabbata cewa acikin littafamsu ne to 'Yan Hakika sune gangariyyar 'Yan Tijjaniyya sauran kuma basa bin asalin tijjaniyyar.
3. Idan kuma maganar malaman mu ta biyu itace gaskiya cewa 'Yan Hakika ba 'Yan Tijjaniyya bane to wadancan sune 'yan Tijjaniyya kenan, Yan Hakika kuma suna batawa wadancan suna.
Wannan shine gaskiyar magana.
In Zaka Fadi Fadi Gaskiya.....
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter