Shin larabci shine Yaren 'yan Aljannah farisanci kuma yaren 'yan Wuta?
1- Ni a ganina wannan baya daga cikin matsalolin mu da har za a tsaya ana hujjatayya tsakanin mu akan wannan mas'alar, kuma koma da wani yare ne za ayi amfani da shi a yinin qiyamah to abinda ake bukata a wurin ka shine imani da wannan rana ta karshe, kayi aiki domin samun kyakkyawan sakamako a wannan ranar, ko kuma kaki yin aiki ka samu munmunan sakamako.
Allah Madaukaki cikin S. Najmi Ayah ta 31 yace:-ولله ما فى السموات وما فى الأرض ليجزى الذين أسآءوٱ بما عملوٱ ويجزى الذين أحسنوٱ بالحسنى*
Kuma abinda yake cikin sammai da kasa na Allah ne domin ya sakankawa wadanda suka munana da abinda suka aikata kuma ya sakankawa wadanda suka kyautata da abu mafi kyau.
A can Suratu Yunus Ayah ta 25-26 sai yace:-
للذين أحسنوٱ الحسنى وزيادة ولا يرهق وجوههم قتر ولا ذلة أولئك أصحاب الجنة هم فيها خالدون* والذين كسبوٱ السيئات جزآء سيئة بمثلها وترهقهم ذله ما لهم من الله من عاصم كأنمآ أغشيت وجوههم قطعا من الليل مظلما أولئك أصحاب النار هم فيها خالدون*
Allah ya azurtamu da samun aljannar firdaus ya nesantar damu daga wuta.
Ameen.

2- An yiwa Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah (Allah ya jikan sa) cikin Majmu'ul fatawa a 4/167 tambaya irin wannan akan wani yare ne Ubangiji zai yi magana da mutane a ranar da za a tada su? kuma shin ya tabbata larabci shine yaren 'yan Aljannah farisanci kuma yaren 'yan wuta?
Sai Shaikhul Islam ya da magana kamar haka:-
((الحمد لله رب العالمين)): لا يعلم بأى لغة يتكلم الناس يومئذ، ولا بأي لغة يسمعون خطاب الرب جل وعلا، لأن الله تعالى لم يخبرنا بشىء من ذلك، ولا رسوله عليه الصلاة والسلام- ولم يصح أن الفارسية لغة الجهنميين ولا أن العربية لغة أهل النعيم الأبدى، ولا نعلم نزاعا فى ذالک بين الصحابة رضى الله عنهم- بل كلهم يكفون عن ذلك.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin duk abinda ba Allah ba: Ba a san wani yare da mutane za suyi magana da shi a wancan lokacin ba, kuma ba a san yaren da za suji maganar Ubangiji mai girma da buwaya ba, domin Allah Madaukaki bai bamu labarin komi game da haka ba, haka ma Manzon sa tsira da Aminci su tabbata gare shi. Sannan bai inganta ba cewa farisanci ne yaren 'yan jahannama ba, haka ma larabci cewa shine yaren 'yan Aljannah, kuma bamu san sabani cikin haka tsakanin sahabbai Allah ya kara mu su yarda ba, a gskia ma dukkan su suna kame bakin su game da haka.

Bayan Shaikhul Islam ya ambato maganganun mutane akan cewa larabci yaren 'yan Aljannah, farisanci ko siryananci yaren 'yan wuta sai yace:-
وكل هذه الأقوال لا حجة لأربابها، لا من طريق عقل ولا نقل، بل هى دعاوى عارية عن الأدلة، والله- سبحانه وتعالى- أعلم وأحكم.
مجموع الفتاوى لابن تيمية 4/167.
Kuma dukkan wadannan maganganu ba hujja ce ga masu fadanta ba, ta hanyar hankali ko naqaltowa, kawai rayawace wofantacciya daga dalili. Allah shine mafi sani

3- Idan wani yace to ai Tabarany cikin Mu'ujamul kabeer da Hakim cikin Almustadrak da Baihaqi cikin Shu'abul Iman sun ruwaito daga Dan Abbas cewa Manzon Allah mai tsira da Aminci yace:-
أحبوا العرب لثلاث: لأني عربي، والقرآن عربي، وكلام أهل الجنة عربي.
A wannan hadisin Manzon Allah ya tabbatar larabci shine yaren 'yan Aljannah to sai ace da shi wannan hadisin hadisi ne maudwu'i, watau hadisi ne na karya. Duba Silsilah Addwa'ifah lambar hadisi 160.

4- Maluma kan ce duk abinda da sanin sa ba zai amfanar da kai ba ba kuma zai cutar da kai ba to bai kamata ka mai da hankali wajen sanin shi ba tunda ba shi da fa'idah, sannan yaren 'yan Wuta ko 'yan Aljannah kamar yadda muka yi bayani a baya ba shine mai muhimmanci ba, sai dai kokarin aikata Alkhairi dan samun Aljannah da kuma nisantar sharri don kubuta daga Wuta.
Allah ya mana rahama.