Kamar yadda aka sani, 'Yan Kungiyar Salafiyyun suna jaraba mutane ta hanyar tambayarsu a game da wani malami, in mutum ya yabi malamin to ya zama SALAFIY (BASALAFE) in kuma ya nuna bai san shi ba to ba Salafiy ba ne, in kuma ya soki malamin to ya zama Hizbiy wato Dan Bidi'a.
To an tambayi Sheikh Saleh Al- Fauzan a kan wannan aiki kamar haka:
فضيلة الشيخ - وفقكم الله - هناك ظاهرة عند بعض الشباب وهي الامتحان بالأشخاص ، فإن وافقته فأنت من أهل السنة وإن خالفته فأنت مبتدع ، فما النصيحة في ذلك؟
Ya Sheikh, - Allah ya sa ka dace – akwai wata dabi'a da ta bayyana a wajen wasu matasa, ita ce: yin Jarabawa wa mutane da wasu mutane, in ka goyi bayan mutumin da aka jarabaka da shi to kai Ahlus Sunna ne, in kuma ka saba masa to kai dan bidi'a ne. to menene nasiha a kan haka?
Sai Sheikh ya ce:
ج - النصيحة أن نقول من وافق الكتاب والسنة فهو من أهل السنة دون النظر إلى الأشخاص إلا محمد صلى الله عليه وسلم , نحن لا نتبع إلا رسول الله صلى الله عليه وسلم ( لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة ) وأما غيره فمن اتبعه اقتدينا به ومن خالفه فإننا نخالفه , فالمتَّبَع هو رسول الله صلى الله عليه وسلم .
ولهذا يقول شيخ الإسلام رحمه الله : من زعم أن شخصا يجب اتباعه غير الرسول صلى الله عليه وسلم فإنه يستتاب وإن تاب وإلا قُتِل ,لأنه أثبت أن هناك من يُتبَع غير الرسول صلى الله عليه وسلم , فلا يُتبع إلا من اتبع الرسول صلى الله عليه وسلم , ولا نمتحن الناس بالأشخاص وإنما نمتحنهم بالكتاب والسنة , واتباع الرسول صلى الله عليه وسلم
إذا يبغى تمتحنه بشخص امتحنه بالرسول صلى الله عليه وسلم لأنه هو الذي يجب اتباعه والإقتداء به . نعم
"Nasiha sai mu ce musu: Duk wanda ya dace da Littafin Allah da Sunna yana cikin Ahlus Sunna, BA TARE DA AN LURA ZUWA GA WASU MUTANE BA, SAI DAI MANZON ALLAH (SAW) KAWAI. Mu ba ma bin kowa sai Manzon Allah (saw):
"Hakika kuna da koyi mai kyau a game da Manzon Allah".
Amma waninsa, duk wanda ya bi shi sai mu yi koyi da shi, wanda kuma ya saba masa sai mu saba masa. Wanda ake bi kawai shi ne Manzon Allah (saw).
Saboda haka ne Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
"Duk wanda ya raya cewa: akwai wani mutum da ya wajaba a bishi ba Manzon Allah (saw) kawai ba, to za a nemi ya tuba, in ya tuba shi kenan, in kuma yaki tuba a kashe shi".
Saboda ya tabbatar da cewa; akwai wani da za a bi bayan Manzon Allah (saw).
Don haka babu wanda za a bi sai wanda ya bi Manzon Allah. Kuma BAI HALATTA MU JARABA MUTANE DA WASU MUTANE BA, a'a, zamu yi musu jarabawa ne da Littafin Allah da Sunna, da biyayya ga Manzon Allah (saw).
Idan yana so ka jaraba shi da wani mutum to ka jaraba shi da Manzon Allah (saw), saboda shi ne wanda binsa da koyi da shi yake wajaba".
Saurari maganarsa ta nan:
http://
Wannan shi yake tabbatar maka da rashin halaccin abin da 'Yan Kungiyar Salafiyyun suke yi NA YIN JARABAWA WA MUTANE DA WANI MALAMI KO WANI MUTUM DABAN, duka a matsayin BIN MANHAJIN SALAF. Lallai wannan BIDI'A NE, saboda babu wani dalili na Shari'a da ya yi nuni a kan haka, kuma ya saba da Qur'ani da Sunna da Manhajin Ahlus Sunna
