MATSALOLIN SOCIAL MEDIA
Mal. Ibrahim isah katsina
Mutane na amfani da social media ba tare da kiyaye ka'idojinta ba, social media na da nata ka'idojin {ethics}. Kafin mutane su fara amfani da ita ya kamata su san wadannan ka'idojin.misali kamar yadda aikin jarida, aikin radio da television suke da ka'ida, haka itama take da nata .
Matsalolin social media sun hada da:
▪Mutane sukan yada labari ta social media wadanda basu da asali ko tushe ballantana makama, kuma cikin dan karamin lokaci kaga labarin ya yadu duk duniya gaba daya.
▪Mutane sukan yada labarai masu tada hankalin al'umma ta social media, za kaga wani abin tada hankali ya faru a wani wuri kamar; gobara ko hatsari, memakon su taimaka wajen kai dauki, a'a sai kaga sun tsaya daukar hotuna da video su yada wa duniya ta gani.
▪Hotuna da video da mutane ke daurawa a social media suma matsala ce sosai, domin yawan cin wadannan hotunan da videos din bai kamata ana dora su akan social media ba, domin sun saba ma shari'ar musulunci. Kuma nan gaba zasu iya zama matsala ga wadanda aka dauki hotunan su ko videon su.
▪Masu kallo ko sauraro ko karatu {audience} a social media suna da tasirantuwa da abinda suka gani a social media, amma da yawan masu yada abubuwa ta social media basa la'akari da komai sai yada abinda yayi musu dadi.
▪Social media ta zama hanyar cin mutuncin masu mutunci, ta yadda zaka ga wasu sunyi shigar burtu domin cin mutuncin wasu ko dai a siyasance ko ma a addinance domin biyan bukatansu.
▪Nuna tsaraici, mutane suna yada tsiraici ta hanyar social media ta inda zaka ga ana tasa hotunan 'yan mata kalakala ga su nan ba adadi.
▪Social media na taimakawa wajen yada fasadi, ta kasance wata hanya ce da mutane ke mu'amala da tasabawa shari'ar musulunci. Misali zaka ga matar aure tana mu'amala da wasu mazan, haka suma mazan zaka ga suna mu'amala da matan harda matan aure.
▪Social media na taimakawa wajen yada kururuwar 'yan cin dan adam, wanda wannan yakan haifar da matsaloli ga rayuwar musulmai kamar 'yancin mata, auren jinsi da sauransu.
▪Social media na cinye lokacin mutane ba tare da sun sani ba, ta inda zaka ga sun bar abubuwa masu mahimmanci a rayuwarsu ta duniya da lahira.
▪Social media na haifar da gaba, kiyayya da rashin son juna, ta inda mutane ke bayyana ra'ayinsu wanda wannan yakan jawo rashin son juna da haifar da fitina ga al'umma.
▪Kallace-kallace a social media, kamar You tube ko Instagram, na ba mutane damar kallon ko wadanne irin fina finai da basu dace ba ko da a al'adance balle kuma a shari'ance.
▪Sauraron wakoki, social media wata hanya ce da mutane ke jin wake-wake marasa amfani a duniya da lahira, zaka ga mafi yawan masu yin waka ta zamani, social media ce hanyar yada wakokin su a yau.
▪Social media ta kara haifar da matsala ga ilmi, ta yadda mugudin jarabawa tayi matukar karuwa. Makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da dalibai suna amfani da ita wajen yada tambayoyin da za'a yi wa masu jarabawa tun kafin lokacin jarabawar.
▪Social media tana taimakawa mutane iri-iri akan yada harkokinsu da ayyukansu na sharri duka. Kamar masu zinace-zinace, masu luwadi, masu madigo, 'yan kwallo, 'yan cha-cha, 'yan club da sauransu. Wadannan munanan ayyukan suna ta karuwa a cikin al'umma ta hanyar social media.
▪Masu garkuwa da mutane {kidnappers} suna amfani da hanyar social media wajen cimma muna nan ayyukansu a cikin al'umma ta yadda suke gano inda suke ta hanyar amfani da goggle map. Ko kuma suma mutane da kansu suke taimakawa ta hanyar cewa a taimaka musu da addu'a ko suna waje kaza.

Ina rokon Allah ya karemu Ni da Ku daga barnar da suke cikin social media.