KWARJININ SHUGABA
Babbar manufar Ilhadin zamani ita ce 'YANCI da SAKEWA A RAYUWA, ta hanyar fita daga duk wani qaidi na wata doka da tsari na hukuma ko Shari'a ta Addini, da fita daga "qiyam" da manyan siffofi na gari da kyawawan dabi'u.
Wanda sakamako da tasirin haka ya haifar da zubar da kimar manyan mutane da jagororin al'umma; Shugabanni da Malaman Addini masana Shari'a, wadanda suka siffantu da ingantaccen ilimi da imani. Alhali hakan ya saba ma "qiyam" da kyawawan dabi'u, saboda a hankalce babu yadda za a yi rayuwa ta inganta matukar babu jagoranci. Jagoranci kuwa ba ya tsayuwa da kafafunsa matukar ba shi da kwarjini da kima a idon mutane.
Tsarin shugabanci da jagoranci abu ne da Allah ya sanya shi cikin halittar dukkan rukunin halittu masu rai, shi ya sa hatta dabbobi za ka samu suna tafiya ne a tsakaninsu karkashin jagoranci. Masana dabi'ar dabbobi sun tabbatar da haka.
Wannan ya sa Shari'a ta yi tanadi mai inganci don kare kwarjinin shugaba, ta hana kalu-balantarsa a kan laifukansa balle kuma fito-na-fito da shi, sai dai Nasiha ta hanya mafi dacewa a kebance ba a bainar jama'a ba.
Alal hakika abin da muke gani a wannan zamani na zubar da kima da kwarjinin jagororin al'umma; shugabannin hukuma, sarakuna da malaman Addini abu ne da ya saba ma fidira da hankali da Shari'ar da Allah ya saukar ma bayinsa. A yau al'umma ta wayi gari babu wani da yake da matsayi da kwarjinin da zai samu kariya ga mutuncinsa, kowa bai wuce a fito a yi masa zigidir a cire masa duk wata rigar girma da mutunci da kwarjini ba. Alhali zubar da kimar shugabanni hanya ce ta lalata Duniyar mutane da haifar da zaman rashin tabbas da rashin tsaro da aminci a cikin al'umma, kamar yadda zubar da kimar Malamai yake kai wa ga lalata Shari'a.
Shi ya sa Malamai suka ce; zubar da kimar shugabanni da Allah ya ba da jagorancin al'umma a hanunsu da ci masu mutunci ya fi yi ma wani farar hula hakan girman laifi, saboda hakan yana hukunta a wulakanta su, a zubar da kwarjini da suke da shi a idon mutane, daga nan kuma hakan ya haifar da rudu da rudani, a rasa tasirin shugabancin nasu, ta hanyar yi musu rashin da'a, har ya kai ga yi musu bore da tawaye, abin da zai haifar da rashin zaman lafiya a cikin al'umma, a samu rashin tsaro da zai kai ga hasarar rayuka da dukiyoyi da keta alfarman mata da kananan yara.
Kamar haka zubar da kimar Malamai da ci musu mutunci, abu ne da yake kai wa ga kaurace musu da jefar da maganganunsu na bayanin Shari'a da sharhin Addini, daga nan sai jahilci ya yadu a cikin al'umma, sai hasken Addini da Shari'a ya dusashe, sai badala da keta Shari'a da rayuwar 'yanci da ilhadi da holewa ta bayyana, shi kenan sai Addini ya tozarta ya lalace a tsakanin al'umma.
Wannan duka sakamako ne na wannan Ilhadin zamani da muke gani, na yakar Addini da "qiyam", daga karshe a koma rayuwar dabbobi babu mai tsawatarwa, rayuwa maras manufa kawai sai neman biyan sha'awan baki da farji ta kowace hanya, sai a wayi gari mai karfi kwace nama, sai ta'addanci ya watsu a cikin kasa, tun da an zubar da kimar shugabanni da malamai masu dauke da Shari'a da Addini, an yi gari babu mai fada aji.
Saboda haka, zubar da kima da kwarjinin shugabanni da malamai lalata Duniya da Addini ne. Saboda Duniya tana dadi ne da da'a ma shugabanni kamar yadda Addini yake inganta da biyayya ga Malamai.