Subscribe Our Channel

Manhajin 'Yan Bidi'a ne, su kirkiri ra'ayi su sanya shi a matsayin wajibi a cikin Addini, suna kulla soyayya da kiyayya a kansa, suna zargin wanda ya saba musu a kansa, kai har su fasikantar da shi su bidi'antar da shi, ko kuma su kafirta shi in masu kafirtawa ne, kamar yadda Khawarijawa da Rafidha 'Yan Shi'a da sauransu suke yi.

Amma Ahlus Sunna ma'abota Sunna da Ilimi gaskiyar da ta zo a cikin Qur'ani da Sunna suke bi, ba sa kirkirar bidi'a, kuma ba sa bidi'antarwa ko kafirta wanda ya saba musu idan ya kasance mai ijtahidi ne ko mai kuskure ko mai Taqlidanci, ko da kuwa shi yana kafirta su yana halasta jinanensu, - kamar yadda Sahabbai ba su kafirta Khawarijawa ba, duk da cewa; suna kafirta Sayyidina Usmanu (ra) da Sayyidina Aliyu (ra) da wanda yake sonsu, kuma suke halasta jinanen Musulmai da suka saba musu -, a'a, Ahlus Sunna uzuri suke yi masa, saboda Allah ya yi afuwa ma wannar al'umma a kan kuskurenta ko mantuwa.

- Ibnu Taimiyya cikin Fatawa (19/ 212), Jami'ul Masa'il (5/ 122)

Saboda haka nake nasiha wa 'yan uwana Ahlus Sunna a kebance, da sauran Musulmai gaba daya, mu nisanci wajabta abu ba tare da Nassin Qur'ani ko Hadisi ko Ijma'i ba, sa'annan mu zo muna bidi'antar da mutane a kansa. Kuma mu zama masu uzuri ma wanda ya afka cikin bidi'a bisa ijtihadi ko jahilci ko taqlidanci, saboda shi mai uzuri ne a wajen Allah Mai rahama.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter