Ingantaccen Addini shi yake warware dukkan matsalolin rayuwa, kamar matsalar mummunar Aqida ko jahilci, ko miyagun dabi'u da munanan halaye ko talauci da karayar tattalin arziki ko cututtuka, ko matsalolin zamantakewa na yaki da rarrabuwan kawuna da sauran damuwowi.
In ka dauki matsalar munanan Aqidu, za ka samu rashin ingantaccen Addini da Aqida da lalacewarsu shi yake lalata dukkan sauran lamuran rayuwa ta Duniya da Lahira, shi yake janyo lalacewar halaye da dabi'u, ya janyo yake - yake, da fadace - fadace da rarrabuwar kai, mutane su rarrabu gida - gida, kungiya - kungiya, dukkansu kuwa a karkace suke sai dai wadanda suke kan ingantaccen Addini da Aqida.
Da yawa daga cikin mutane Shaidan ya yi wasa da hankulansu, inda ya yi wasa da hankulan Mushrikai, wasu suka bauta ma Gumaka, wasu Taurari, wasu Kabarburan Shehunnai da Waliyyai, duk da cewa; sun yarda Allah ne shi kadai Ubangiji Mahalicci, amma suka kasa bauta masa shi kadai.
Wasu kuma da Shaidan ya tashi yi musu fitsari sai ya yi musu a tsakar ka, inda suka rungumi Ilimin Falsafa (Philosophy) da ikrarin bin Ilimi da Hankali, sai ga su sun zo mana da bata mafi girma, inda suka kore samuwar Allah Madaukaki, balle su yi Imani da Manzanninsa da Littatafansa, suka karyata abubuwa na gaibi, suka karyata Ayoyin Allah, alhali a zuciyarsu sun san karya suke yi. Sai suka koma bautar Dabi'a (Nature), a karkashinta suka koma bin sha'awowin ransu, suka ki bin Shari'o'in Addini da Kyawawan Dabi'u na mutuntaka, sai suka zama tamkar dabbobi, ba su da manufa sai sha'awar zuciyoyinsu da bakunansu da farjojinsu da sha'awar rayuwa kawai.
{وَقَالُوا مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا يُهْلِكُنَا إِلَّا الدَّهْرُ } [الجاثية: 24]
Amma Addinin Muslunci kuwa shi ya fitar da mutane daga dimuwa da rudu da suke ciki, ya fitar da su daga duhun jahilci da kafirci da zalunci da ta'addanci zuwa ga hanken Ilimi da Imani da adalci da rahama da dukkan alkhairai da rayuwa mai dadi mai manufa.