*_GYARUWAR MACE KO 'BACIN TA YANA DA TASIRI MAI QARFI AKAN MIJIN TA*_
Imaam Hasanul-Basari Allah yai masa rahma ya fada cewa:
"Na tsaya wajen wani mai siyar da tufafi a Makkah da nufin siyan kaya a wajen sa,
sai ya fara rantse-rantse da yabon kayan sa, sai nace: siyayya a wajen mutum irin wannan bai kamata ba, sai na je wajen wani na siya.
sai ya fara rantse-rantse da yabon kayan sa, sai nace: siyayya a wajen mutum irin wannan bai kamata ba, sai na je wajen wani na siya.
Bayan shekara biyu na kuma koma wa aikin hajji, da na sake tsayawa a wajen wannan mai sai da tufafi sai ban ji yana irin wannan kodawar da rantse-rantsen da yake yi ada ba.
Sai nace da shi: Ashe ba kai ne mutumin nan dana ta6a tsayawa wajen sa ba a shekarun baya?
Sai mutumin yace: Na'am, Ni ne!
Sai nace da shi: To amma me ya canja ka zuwa abin da nake gani yanzu? Ban ga kana kod'a hajar ka ba kuma ban ga kana rantse-rantse ba!
Sai mutumin yace: Na kasance ina da wata mata; idan na kawo mata abu kadan sai ta qasqantar da abin, idan kuma na kawo mai yawa sai ta qanqantar da shi, sai Allah yai mata rasuwa, sai na auro wata matar, Idan zan fita zuwa kasuwa sai ta riqe tufafi na sannan tace: Ya kai wane kaji tsoron Allah! Kada ka ciyar damu face sai da abu mai kyau na halal, idan ka zo mana da kadan zamu yawaita shi, idan ma baka zo mana da komi ba zamu taimaka da tufafi da muke saqawa mu siyar, ba zamu ci haramun ba
Allahu Akbar! Lallai acikin wannan akwai darasi mai girman gaske da mataye ya kamata su dauka wajen sauya halayen mazajen su gami da dora su a hanya a duk lokacin da suka karkace.
Ita mace Allah bai halicce ta da qarfi irin na da namiji ba, amma ya halicce ta da qarfin tasiri irin wanda da namiji bai da shi.
Irin wannan tasirin ne waccan matar ta farko tayi amfani da shi wajen jefa mijin ta cikin halaka na yin rantse-rantse a cikin kasuwancin sa, sakamakon duk abinda ya kawo mata komin yawan sa bata yi masa kallon mutunci balle fa tayi godiya, hakan ya sanya shi tsunduma cikin irin wancan laifi wanda babban laifi ne da kan jefa bawa cikin fushin Allah da har zai kai ga Allah ba zai yi duba ko yin magana da wanda yake irin wannan halayya a ranar Al-Qiyamah ba, kuma ba zai tsarkake shi daga azaba ba.
Har ila yau, da Allah ya bashi wata matar ta kirki, irin wannan tasirin ne itama tayi amfani da shi wajen ceto shi daga halakar da matar sa ta farko tayi sanadin jefa shi, ta hanyar nuna masa girman jin tsoron Allah a cikin neman sa, ta kuma nuna masa godiyar ta ga duk abinda ya kawo mata komin qanqantar sa, tare da nuna masa koda ma bai samo ba kada ya damu ita zata taimake shi daga abinda take yi na sana'a su ci abinci na halal yafi ace ya nemo musu haram sun ci.
Shi ne yake fadawa Imaam Hasanul-Basari cewa wannan ne fa dalilin daya sa kaga na canja daga rantse-rantsen da nake yi a lokacin baya.
Allah sarki! Ina ma ace matan wannan zamani suna amfani da qarfin tasirin da suke da shi a wajen mazajen su ta hanyar sauya halayyar su izuwa alkhayri?!
Sai dai kuma kash!!!
Da yawan su sun fi amfani da wannan tasirin ne ma wajen jefa mazajen na su cikin neman qamiya-miya su kawo musu, basu damu ba indai za'a gan su a cikin manya-manyan gidaje suna hawa mota ko saka duk irin suturar da suke so na kece raini.
Da yawan su sun fi amfani da wannan tasirin ne ma wajen jefa mazajen na su cikin neman qamiya-miya su kawo musu, basu damu ba indai za'a gan su a cikin manya-manyan gidaje suna hawa mota ko saka duk irin suturar da suke so na kece raini.
Basu sani ba ko kuma sun manta cewa Annabi SAW ya fada cewa duk tsokar data ginu da haramun to wuta ce tafi dacewa da ita.
Allah nake roko yasa matan wannan zamani zu ji kuma su yi koyi da wannan mata ta biyu ga mazajen su.