Subscribe Our Channel

GUZURIN MASOYA  A KAN GINA SOYAYYA BISA QAUNA TA GASKIYA

An yi wani mutum ya auri wata kyak-kya'war mace. Wace take da kyau so sai da so sai kuma yana matuqar qaunar matar qauna mai tsanani.

Kawai sai cutar fatar jiki ta kama matar fatar ta tariqa lalacewa har dai a ka wayi gari fatar ta ta yaqune so sai.

Sai matar ta riqa baqin ciki kasan cewar kyawun ta  duk ya tafi.

Sai dai kuma a lokacin da ta haďu da wan nan cutar mijin ba ya gari,domin yayi tafiya zuwa wani gari.
Shi kuma mijin nata sai yayi hatsari a lokacin da yake kan hanyar sa ta dawowa gida,sai wannan hatsari da yayi ya zama sanadiyyar rasa ganin sa domin makan cewa yayi.

Haka ma'auratan suka riqa rayuwar su har tsawon wani lokaci.

Ita ma'tar ta rasa kyawunta,shi kuma mijin ya zama makaho Kuma bai san cewa matar sa ba tada kyau ba a yanzu

a haka su kayi ta rayuwa mai tsayi. Kowanne daga cikin su yana matuqar girmama d'an uwan sa.

Domin mijin yana qaunar ta qauna mai tsanani kuma yana girmama ta kamar yadda yake girmamata a da.

Ita ma matar tana girmama shi kamar yadda take girmama shi a da.

Har izuwa lokacin da matar ta mutu.‎‏

Mijin nata yayi matuqar baqin ciki da rasuwar matar sa, kuma yayi mata addu'a so sai da so sai.

Bayan anyi jana'izar ta sai mijin yaje wani guri ya zauna shi kaďai yana tuna ni.

Sai wani yazo yace masa ya naga ka zauna kai kaďai alhãli matar taka ta rasa kyawun ta tun da daďewa?

Sai mijin ya kalle shi sannan yace: ai nima ba makancewa nayi ba.
Ballan tana kace ban sani ba. na gaya ma jama'a cewa na makan ce ne kawai domin ba naso matata taga ina kallon ta a cikin mummunar kamar da take ciki.

Don na san idan taga ina kallon ta a wannan kaman ni to haka zai riqa damun ta har ya iya sãta cikin wani mugun hãli da zai cutar da ita.

Wannan shine dalilin da yasa nace na makan ce. Alhãli ban makan ce ba.
Kuma na riqa mu'amala da ita kamar yadda nakeyi a da.

SHIN "YAN UWA YA KUKE GANI DA AN GINA WAN NAN SOYAYYAR A KAN KYAWU???
Mal. Ibrahim Nuhu

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter