Subscribe Our Channel

GULUWWI A KAN WANI MALAMI KO YI MASA JAFA'I DABI'A CE TA 'YAN BIDI'A DA MABIYA SON RAI

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
إن الرجل العظيم في العلم والدين، من الصحابة والتابعين ومن بعدهم إلى يوم القيامة، أهل البيت وغيرهم، قد يحصل منه نوع من الاجتهاد مقرونا بالظن، ونوع من الهوى الخفي، فيحصل بسبب ذلك ما لا ينبغي اتباعه فيه، وإن كان من أولياء الله المتقين.
ومثل هذا إذا وقع يصير فتنة لطائفتين: طائفة تعظمه فتريد تصويب ذلك الفعل واتباعه عليه، وطائفة تذمه فتجعل ذلك قادحا في ولايته وتقواه، بل في بره وكونه من أهل الجنة، بل في إيمانه حتى تخرجه عن الإيمان. وكلا هذين الطرفين فاسد.
والخوارج والروافض وغيرهم من ذوي الأهواء دخل عليهم الداخل من هذا. ومن سلك طريق الاعتدال عظم من يستحق التعظيم، وأحبه ووالاه، وأعطى الحق حقه، فيعظم الحق، ويرحم الخلق، ويعلم أن الرجل الواحد تكون له حسنات وسيئات، فيحمد ويذم، ويثاب ويعاقب، ويحب من وجه ويبغض من وجه. هذا هو مذهب أهل السنة والجماعة، خلافا للخوارج والمعتزلة ومن وافقهم.
منهاج السنة النبوية (4/ 543 - 544)

"Lallai babban Mutum a Ilimi da Addini, daga cikin Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka zo a bayansu, har zuwa Ranar Qiyama, Ahlul Baitin Annabi (saw) da wasunsu, ta yiwu nau'i na Ijtihadi ya faru daga wurinsa, wanda yake hade da zato, da kuma nau'i na boyayyen son rai, sai a samu wani abu da bai kamata a bi shi a kansa ba ya faru, ko da kuwa ya kasance yana cikin Waliyyan Allah masu Taqwa.

Idan irin wannan ya faru, sai fitina ta faru wa bangarori guda biyu;
1- Bangare suna girmama shi, SAI SUYI KOKARIN GYARA WANCAN AIKI NASA, DA KUMA BINSA A KANSA.
2- Daya bangaren kuma SAI YANA ZARGINSA, SAI YA MAYAR DA WANCAN KUSKURE NASA A MATSAYIN ABIN SUKA GA WALITTAKARSA DA TAQWARSA, kai har da'arsa ga Allah da kasancewarsa Dan Aljanna, kai, har su yi suka cikin Imaninsa har su fitar da shi daga cikin Imani. Alhali kowanne bangare daga bangarorin guda biyu batacce ne (Mabarnaci).

Khawarijawa da Rafidha ('Yan Shi'a) da wasunsu daga cikin mabiya son rai kaso na wannan ra'ayi ya shigesu.

Amma WANDA YA BI HANYAR DAIDAITUWA (MUWAZANA), ZAI GIRMAMA DUK WANDA YA CANCANCI A GIRMAMA SHI, KUMA ZAI SO SHI YA JIBINCE SHI, KUMA ZAI BAI MA GASKIYA HAKKINTA, ZAI GIRMAMA GASKIYA, YA TAUSAYA WA BAYIN ALLAH, KUMA ZAI SAN CEWA; LALLAI MUTUM GUDA, ZAI KASANCE YANA DA KYAWAWAN AIYUKA KUMA YANA DA MUNANA, DON HAKA ZA A YABE SHI A KAN KYAWAWA, A ZARGE SHI A KAN MUNANA, AYI MASA SAKAMAKO A KAN KYAWAWA AYI MASA UQUBA A KAN MUNANA, A SO SHI TA WATA FISKA, A K'I SHI TA WATA FISKAR.

WANNAN SHI NE MAZHABAR AHLUS SUNNATI WAL JAMA'AH, SABANIN KHAWARIJAWA DA MU'UTAZILA DA WANDA YA DACE DA SU A KAN HAKA".

ABIN LURA:
1- Gaskiya tana tsakanin bata guda biyu ne, don haka hanya madaidaiciya tana tsakanin Guluwwi da Jafa'i.
2- Mazhabar Ahlus Sunnati wal Jama'a (Salafiyya ta Hakika) shi ne MUWAZANA.
3- Dukkan Muminai (duk Musulmin da ba Munafuki ba), ba a yi musu kiyayya, a barranta daga garesu gaba daya, a'a, kowa za a so shi ne gorgodon kyawawansa, kuma za a ki shi a kan munanansa.
4- Manhajin Salafiyyun, na Jarhi da hukunci ga mutane, asalinsa daga Manhajin Khawarijawa da Mu'utazilawa ne, wadanda suke kore MUWAZANA.
5- Abin da muke gani a kan Sheikh Albaniy Zaria, na Guluwwi daga wasu mutane ('Yan Kungiyar SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA), da kuma Jafa'i daga wasu (Salafiyyun), yana cikin wannan nau'i.
SABODA HAKA MU BA MA CIKIN WADANDA SUKE GIRMAMA MALAM ALBANIY ZARIA DA HAR ZA MU CE; DUKKAN ABIN DA YA YI DADAI NE, HAKA KUMA BA MA CIKIN WADANDA ZA MU YI TA SUKANSA MUNA ZARGINSA A KAN KUSKURENSA, A'A, MUNA SONSA, MUNA YABONSA A KAN KYAKKYAWANSA, KUMA MUNA YI MASA FATAN AFUWA DA GAFARA A WAJEN ALLAH A KAN KURAKURENSA, AMMA BA ZA MU BI SHI A KANSU BA.

SABODA HAKA WANNAN SHI NE MATSAYA MAI KYAU A GAME DA KURAKURAN KOWANE MALAMI A NIGERIA, DA MA KO'INA A FADIN DUNIYA.

Dr Aliyu Muh'd Sani

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter