Subscribe Our Channel

*DAME ZA MU FUSKANCI RAMADAN ?*
_*(Rubutu na Daya)*_

بسم الله والصلاة والسلام على رسول الله وعلى آله وصحبه أجمعين

Bayan sanya sunan Allah, da salati ga Fiyayyen Halitta da Alayensa da Sahabbansa baki daya, Bayan haka.

'Yan Uwa taken wannan rubuta nawa shine *DAME ZA MU FUSKANCI RAMADAN ???*

Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da ya kamata ace kowane Musulmi ya tambayi kansa, domin yin tanadi ga zuwan wannan wata mai alfarma da daraja.

Magabata na qwarai koda yaushe babban abin dubinsu shine Gobensu (Alqiyama) shi yasa suke shiri domin riskuwarta ta hanyar zage damtse wajen yin Ibadodi.
Sahabbai sun kasance dayan su kanje kasuwa yayi dako a biyashi ba domin ya ci ba sai don kawai ya kawo Sadaka wajen Manzon Allah (SAW). Wannan na nuna mana yadda Sahabbai suke da kwadayin Ibada.

Mu kuma ayau babban abinda muke duba Duniyar nan kadai, shiyasa mafi yawancin mu babu wani tanadi da muka yiwa Goben mu.
Babban fadi - tashin mu yana ga lamurran duniya.

A shekaru uku zuwa hudu da suka gabata wata babbar Supermarket ta shelanta za ta saki garabasa inda ta ayyana rana da lokaci, ta sanya sharadin garabasar shine za'a ba da daqiqa daya duk abinda ka fito dashi daga cikin supermarket din ya zama naka. Sai aka samu wani saurayi cikin  daqiqa daya dinnan ya fito da kayan da kudinsu sun wuce misali saboda tsadansu. Da aka tambayeshi ya akayi ya samu damar fito da irin wadannan kaya masu makuden kudi sai yace, tun lokacin da aka bada sanarwar wannan supermarket za ta bada garabasa tun a lokacin kullun sai ya shiga Supermarket din ba domin yayi sayayya ba sai don ya duba ire - iren kayan da keda tsada kuma za suyi masa sauqin dauka a ranar gasar.

*Babban abin Lura a wannan labarin shine:*
Yadda wannan saurayin ya yi shiri na musamman domin haqarsa ta cimma ruwa, wannan fa wani lamari ne na duniya, ina ga wanda ke bidar Aljannah ai min bábi aula yayi shiri domin samunta...

Yau idan akace akwai wani babban bako da zai ziyar ce ka, kakanyi iya yinka wajen shirin yadda za ka tarbe wannan bakon, duk saboda ka dadantawa wannan bakon naka rai.
Kwanaki kadan ya rage Babban Bako ya ziyarce ka me dauke da rahama da gafara shine watan Ramadan shin ko za kayi shiri domin tarbon sa ???

Kafin na shiga kai tsaye kan maudu’in zan so musan wane wata ne watan Ramadan ?

Watan Ramadan shine wata na tara (9) acikin jerangiyar watannin musulunchi, wanda yake tsakanin Watan Sha’aban da Shawwal, kuma shine watan da Allah (SWT) ya wajabtawa musulumi azumtar sa.

*FALALAR WATAN RAMADAN*
Yana daga cikin abunda ke sa mutun yayi shiri kan zuwan wani idan yasan darajar wannan abun da falalarsa.
Ba shakka kuwa watan Ramadan yana dauke da falaloli da dama wadanda ba zasu qirgu ba acikin ayoyin Al-Qurani da Hadisan Manzon Allah (SAW), kadan daga cikin falolinsa akwai:

👉🏽 *ANA BUDE KOFOFIN ALJANNA A KULLE KOFOFIN WUTA A KUMA DAURE SHEDANU*

Ba wani wata daga cikin watanni da ake kulle kofofin wuta a bude kofofin Aljanna a kuma kulle shedanu sai wannan wata mai daraja da falala kamar yadda yazo acikin Sahihaini daga Abu Huraira (RA) Yace:

_“Manzo Allah (SAW) Yace idan Ramadan yazo ana bude kofofin Aljanna, a kulle kofofin wuta a kuma daure shedanu” (Bukhari 1898, Muslim 1079)_

*إذا جاء رمضان فتحت أبواب الجنة , وغلقت أبواب النار , وصُفِّدت الشياطين*

Zan dakata anan, Sai mun hadu *Rubutu na biyu*

✍🏼
Yakubu Ja'afar Abdullah

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter