Subscribe Our Channel

CIKAKKIYAR TATTAUNAWA DA MAL. ADAMU ALIYU MAIGORO DAYA DAGA CIKIN DATTAWAN MALUMAN SUNNAH A NIGEIRA

Wannan tattaunawace da akayi dashi ranar laraba 18/14/2018 a gidansa dake unguwar Rigasa a Kaduna asha karatu da sauraro lfy.

Assalamu Alaikum warahmatullah, To ni dai zaton da nake an haifeni 1938 a garin Maigora dake jihar Katsina, akwai wani sarki da aka nada ance min an nadashi da shekaru ko biyu ne aka haifeni, domin lokacin sunje bikin nadin nasa a Katsina suka dawo an haifeni kuma lokacin an dan dade ba’a nadashi ba an kai wajen shekara biyu.

Naje makarantar Arabiyya a wasu kauyuka daga cikin su akwai Funtua, Dandume, Malumfashi da kuma Yashe, na danje gabas da Kano amman wadannan malaman mu suka daukemu suka tafi damu, da na dawo gidan na dan shiga makarantar boko amman ban dade ba ko firamare (7) ban gama ba, don lokacin aji bakwai ke yi a firamare.

Daga nan na taho Zaria wajen karatu bayan na koma na sake dawowa nayi Diploma, ta fannin karatu iya kata nan indai ba na zaure ba.
Daga cikin malaman da nayi karatu a wurinsu akwai:
Mal. Ibrahim Dan Mal. Audu, Alaramma Mal. Abdullahi Funtua, Mal. Yahuza Zaria, Mal. Shitu Sabon Garin Zaria, Mal. Rabi’u Dattijo Kaduna.
Daga cikin abokanan karatu na akwai:
Mal. Musa Alaramma, Mal. Abdulhamid Alaramma, Mal. Salihu Alaramma, Mal. Umar Sokoto.
Na shiga da’awa a Nigeria tun zamanin Jama’atu, da aka kafa jama’atu wajejen 1963 na shiga jama’atu (J.N.I) a lokacin, muna nan muna yin jama’atu har akayi juyin mulki 1966 bayan anyi juyin mulki daga baya aka zo aka kafa kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa’ikamatis sunnah shima dani akayi, dani aka je har Jos wajen kafa ta.

A yanzu nine mai gabatar da malamai masu wa’azi na kungiyar Izala ta kasa, sannan ni dan majalisar koli ne na kungiyar, sannan mamba na sanya wa’azi tun kafa kungiyar har zuwa yanzu.

Daga cikin wa’azuzzukan da muka fi shan wahala acikin sa akwai wa’azin YALWAN SHENDAM shine muna kan mimbari ana harbin mu aka sassamu wasu, amman Allah bai sa an sameni ba, kuma ‘Yan sanda suka kama wasu amman ni Allah baisa an kamani ba.
Sa wa’azin KURGWI ita ma bata da nisa da YELWAN SHENDAM sai kuma na SAMINAKA shima munsha wahala domin da mukaje an dauko makada akayi ta rikici ni dai na kan minbari ba’ayi wa’azin ba rannan, aka koremu muka koma KADUNA to lokacin Alh. Bala Surajo yaje ya samu shugaban ‘yan sanda na wancan lokacin kwamishina yace su zasu koma SAMINAKA su abinda suke rook kawai a basu ‘yan sanda basa bukatar komai zasu zuba ‘yan agajinsu, Mal. Abubakar Gumi Allah ya jikan rai yace “a’a mu barsu su huta”, a gabana Alh. Bala Surajo yace “a’a malam a lokacin da kake kiranmu da girmanka da komai ba’a son wa’azinka balantana mu yanzu muka taso fa”, a takaice dai muka koma SAMINAKA sati mai zuwa wanda yake shugabancin kidan a wancan lokacin shi kuma yazo yana shugabantar hada lasifukun wa’azi, wani abun mamaki suka fada mana wadanda suka sanya su wannan aikin, akwai wani yana cewa mu rubuta sunayensu mu kace a’a wannan sharrine bai kamata a rubuta shi cikin tarihin ba.

Shawara ga matasa masu tasowa wajen da’awa
Shawara ga kungiyar Izala
Rabuwar kungiyar Izala ba rabuwace ta Akida ba

Domin sauke cikakkiyar hirar sai ka danna link din dake kasa:

http://darulfikr.com/s/45117

#BasheerSharfadi #JibwisNigeria

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter