Subscribe Our Channel

Duk dan bid'ar da bid'arSa bata kai kafirci ba to, ba za a kisa gaba daya ba, za a so shi gwargwadon abinda yake tare da shi na imani da bin Annabi, sannan aki shi gwarwadon abinda yake tare da shi na bid'ah da sabo.

Wannan asaline da Ahlus Sunnati Wal Jama'ah suka hadu akai, Khawarij da da Mu'utazilah da wadanda suka bi ManhajinSu suka sabawa Ahlus Sunnah akan hakan.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yace:
وإذا اجتمع فى الرجل خير وشر، وفجور وطاعة، ومعصية وسنة وبدعة، استحق من الموالاة والثواب بقدر ما فيه من الخير، واستحق من المعاداة والعقاب بحسب ما فيه من الشر، فيجتمع فى الشخص الواحد موجبات الإكرام والإهانة، فيجتمع له من هذا وهذا، كاللص الفقير تقطع يده لسرقته، ويعطى من بيت المال ما يكفيه حاجته.
وهذا هو الأصل الذى اتفق عليه أهل السنة والجماعة، وخالفهم الخوارج والمعتزلة ومن وافقهم.
مجموع الفتاوى (28/117).
Idan Alkhairi da sharri suka haduwa Mutum, da fajirci da Da'a, da sabo da Sunnah da Bid'ah, to ya cancanci soyayya da jibinta da lada gwargwadon abinda yake tare da shi na Alkhairi, kuma ya cancanci kiyayya da ukuba gwargwadon abinda yake tare da shi na sharri, sai abinda yake wajabta girmamawa da wulakatanwa ya haduwa Mutum Daya, sai wannan da wancan ya hadu gare shi, kamar Barawo Matalaucine, za a yanke hannunSa sbd SatarSa, kuma a bashi abinda zai ishe shi bukatarSa daga Baitul Mali.
Wannan shine Asali da Ahlus Sunnati Wal Jama'ah suka hadu akanSa, Khawarij da Mu'tazilah da wadanda suka dace musu suka sabawa Ahlus Sunnah.

Sbd haka duk dan Bid'ar da bid'arSa bata kai kafirci ba to za a soshi gwargwadon imaninsa, kuma ayi masa kiyayya gwargwadon sharrinSa.

Harta kauracewa dan bid'ah manufar shine ladabtar da shi da yi masa ukuba ko hakan zai sa ya tuba, Sannan kauracwar yana ginuwa ne a bisa lura da maslaha, abinda maslaha ta hukunta shine Addini kuma tafarkin Ahlus Sunnati Wal Jama'ah.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter