Subscribe Our Channel

Tun farko an dauko Sufanci ne daga Zuhudu (gudun Duniya), sai Sufayen suka yi sakaci suka halasta rawa da waka da jin music, sai masu neman Lahira cikin amawa gama garin mutane suka bi su saboda gudun Duniya, sai kuma 'Yan Duniya suka bi su saboda son holewa da cashewa.

Sufaye suna kasa Addini zuwa "Shari'a" da "Hakika", da "zahiri" da "badini", abin da suka dauko daga Kungiyoyin Badiniyya.

Abin nufi da Shari'a a wajen Sufaye shi ne abin da dukkan mutane suka yi tarayya a cikinsa na lamarin Addini, wanda ake dauko shi daga Alkur'ani da Hadisi da Ijma'i, kamar Tsarki, Sallah, Azumi da sauransu.

Don haka ma'abota Shari'a su ne 'Yan Zahiri, wadanda suka kasa su gida biyu:
1- Amawa masu yin Sallah da Azumi.
2- Malaman Shari'a, wadanda ba su san hakika da badini ba, kawai su zahirin Nassoshi suka sani da kuma hukunce-hukuncen Shari'a na Tsarki da Sallah da Azumi.

Amma 'Yan Hakika kuma su ne Sufaye masana badini, wato su ne tatattun Sufaye. Wadanda suka fita daga Shari'a zuwa hakika, duk abin da Shari'a ta wajabta na Tsarki da Sallah da Azumi su ba wajibi ba ne a kansu, haka duk abin da Shari'a ta haramta na Zina da shan giya da aikata alfasha da dukkan masha'a ba haramun ba ne a kansu. Saboda su sun gama Shari'a sun shiga hakika da badini.

'Yan Hakika su ne wadanda suka kai kololuwa a Sufanci, suka samu ilimin "Ludani" ta hanyar "Kashafi", wanda ba a bayar da shi ga waninsu ba. Wannan ilimin shi suke kira "Hakika", ko ilimin "badini" da suke dauko shi daga Allah kai tsaye ba tare da wani dan aike a tsakani ba. Har suke kaiwa matsayin "Fana'i" da ganin  komai abu daya ne, komai ya zama Allah, babu banbanci tsakanin Allah da bawa, Allah shi ne bawa, bawa shi ne Allah.

A wajen Sufaye, Hakika ita ce asali, ta Arifai kenan, Shari'a kuma reshe ce, wato ta Amawa, wadanda hankulansu ba za su iya fahimtar hakikar ba.
Al-Nabulusiy ya ce:
"الحقيقة أصل والشريعة فرعها".

"Hakika ce asali Shari'a kuma reshenta".

Sai ka jefar da Shari'a da Alkur'ani da Sunna kafin ka zama Sufiy na hakika.
Wata rana Abul Qasim Umar Al-Maragiy ya zo wajen Afif Al- Tilmasaniy sai ya ce:
"إن كنت تريد أن تعرف علم القوم فخذ الشرع والكتاب والسنة فلفها واطرحها".
الدرر الكامنة في أعيان المائة الثامنة (4/ 185)

"In kana so ka san ilimin Sufaye to ka dauki Shari'a da Alkur'ani da Sunna ka daure su ka yi jifa da su".

A wajen Sufaye, Hakika wani sirri ne wanda a zahirinsa kafirci ne mai sa a sare kan mutum.
Muhyid Deen Al-Du'amiy ya ce:
"الحقيقة صعبة، فحقائق بدايات الأولياء أصعب من نهاياتهم، ولو أن وليا كاشف الخلق بأقل وأدنى حقيقة من حقائق بدايته لاتهموه بالكفر ولقطعوا وريده".
تكملة الفتوحات المكية (1/ 585)

"Hakika tana da wahala, hakikokin farkon waliyyai sun fi wahala a kan karshensu. Da a ce Waliyyi zai bayyana wa mutane mafi karancin Hakika daga cikin hakikokin farkon walittakarsa to da mutane sun tuhume shi da kafirci, da sun yanke jijiyar wuyarsa".

Saboda haka, manyan Malaman Sufayen boyewa kawai suke yi, saboda in sun bayyana Hakikar za a ce: sun kafirta.

Saboda haka, 'Yan Hakika su ne wadanda suka isa kololuwar Sufanci. Duk wanda bai isa Hakika ba to ba cikakken Sufiy ba ne, bai wuce matsayin amawa gama garin mutane ba.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter