ASALIN UNGUWAR SHARFADI DAKE KANO
Wani mutum mai suna Sharafuddeen yazo daga garin Borno ya zauna a unguwar, Shine dalilin da yasa ake kiran sunan unguwar da sunansa, sai dai a maimaikon Sharafuddeen sai mutane suke cewa Sharfadi.
Bayan shi sai kuma Muhammadu Kuyatu, shima ya tare a unguwar shida jama’arsa.
Akwai wani yanki a unguwar mai suna Madatai ana kiransa haka saboda ada duk itatuwan madaci ne wurin. A da akwai kurkuku mai suna Gidan Ma’aji a wajen ake ajiye mai laifi kafin a yanke masa hukunci, akwai kuma gidan ma’ajin watari.
zuri'ar Malam Kuyatu da kuma mutanen Gamadan na garin Dawakin Kudu sune mafi yawa a unguwar.
Har yanzu ana gudanar da sana'ar Jalala ta Doki a unguwar.
Akwai makarantun ilmi a unguwar, kamar ta marigayi Mal. Sambo Mai Tafsiri, ta marigayi Malam Yahaya Na-Galadima da ta marigayi Mal. Halilu, a yanzu ‘ya’yan wadannan malamai ne suke gudanar da ilmi a makarantun.
A makarantun Islamiyya akwai wadda Malam Ashe ya gina da kuma ta Malam Datti.
Muna addu’ar Allah ya karawa wannan unguwa albarka da kuma cigaba mai dorewa Amin.
www.sharfadi.com