Alhamdulillah, Masha Allah, Laquwwata illa Billah!!!
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Ranar Litinin 9 ga watan afrilu 2018 misalin karfe 10:41 AM Na safe muka bada sanarwar cewa "DARULFIKR.COM NA NEMAN TAIMAKON KUDI DAGA YAN UWA DOMIN CIGABA DA YADA ADDINI". Wannan sanarwa mun sake maimaita ta a ranar Talata 10 ga watan afrilu 2018 da misalin karfe 08:07 AM na safe, tare da bayyana cigaban da aka samu na tallafi daga yan uwa.
Tabbas yan uwa Ahlussunnah sun zaburo, sun tallafawa wannan cibiya kama daga masu turo da dukiyarsu, adduoi na fatan dacewa da ma masu taimakawa wajen yada wannan sanarwa.
Sunnah Kenan...
Hantsi Leka Gidan Kowa .....
Alhamdulillah, tun bayan yin posting dinmu na farko zuwa yau safiyar Laraba @9:55AM mun karbi tallafi daga hannun mutane dai dai har guda dari da 130 sai cikon na 131 shine wanda ya bada $100 ->N35,000 tun Kafin wannan sanarwa, wato asusun mu na farko kenan.
Ga break down na duka transactions din kudin da aka turo mana grouped by amount.
1. Akwai mahaifin wasu yan uwanmu dalibai Ahlussunnah da muke tare dasu a wannan Kafa shi daya tilo ya bada Naira dubu dari hudu da hamsin N450, 000.
Allahu Akbar, Allah ya saka masa da Jannatul firdausi.
2. Akwai wani bawan Allah shima da bai so a bayyana sunan sa ba, shima yayi hobbasa ya bada naira dubu N100, 000.
3. Sannan wani dan uwa abokin mu abokin karatunmu daya bada $100 wato wannan N35,000(ta asusun mu ta farko ) tun ranar jumaa kafin sanarwa ta bayyana.
4. Sauran yan'uwa da suka taimaka, ga kudaden su kamar
N20, 000. X (mutum 1) = N20, 000
N15, 000. X (mutum 1) = N15,000
N10, 001. X (mutum 1) = 10,001
N10, 000. X (mutane 6) = N60,000
N5, 500. X (mutum 1) = N5,500
N5, 000. X (mutane 15) = N75,000
N4, 000 X (mutum 1) = N4,000
N3, 000 X (mutane 8) = N24, 000
N2, 000 X (mutane 17) = N34, 000
N1500. X. (mutane 4) = N6,000
N1, 000. X. (mutane 42) = N42, 000
N900. X. (mutum 1) = N900
N800. X. (mutum 1) = N800
N700. X. (mutum 1) = N700
N500. X. (mutane 12) = N6000
N300. X. (mutane 2) = N600
N360. X. (mutum 1) = N360
N200. X. (mutane 6) = N1200
N100. X. (mutane 3) = N300
N50. X. (mutane 3) = N150
Total muna da kudi Naira dubu dari takwas da casai'n da shida da naira dari biyar da tamanin da tara da digo goma == N896, 589.10
اللّه على ما نقول وكيل.
Muna adduar Allah ya saka muku da Aljannah gaba daya, ya kai cikin mizanin alkhairi, mu kuma Allah ya bamu ikon sauke nauyin da ke kayin mu. Ameen
Sannan duka wadannan mutane 130 muna da list dinsu gaba daya written da sunayen su, sai dai Akwai mutum 13 wadanda Sukayi transfer da payment gateways irinsu remita, Cmobile su bamu da sunayen su amma muna da transactionId din su, account number ko lambar waya.
Sannan duka wannan tallafin an karbe shi ta account din access bank Mai Suna MUBARAK AUWAL idan banda daya na farko ($100 = N35,000) shima daga baya mun dawo dashi cikin account na access bank din.
Sannan bamu karbi ko naira daya hannu da hannu ba face ta account using transfer.
Alhamdulillah yanzu haka tuni mun tuntubi service providers dinmu yanzu haka Darulfikr.com is under virus scan process, nauyin files dinmu yasa zai Dan dau lokaci amma nan da wani kankanin lokaci zasu sake tuntubar.
In shaa Allah zamu sake sanar da ku halin da muke ciki, da duk duk yadda muka yi amfani da kudadenku da abin da yayi saura.
Sannan a taya mu yada wannan sanarwa domin Mun Riga mun samu adadin kudin da muka nema har sun ninka, Saboda sauran mutane su san cewa mun samu da halin da muke ciki.
Jazakumullahu khairan.
Mubarak Auwal
A madadin kwamitin gudanarwa na Darulfikr.com.
11-04-2018 @ 9:55AM
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=611228515898707&id=275478802807015