Subscribe Our Channel

Taskar Zinari //0
.
Sau da dama muna aukawa cikin kuskure acikin Tattaunawa ta addinin ta fuska biyu zuwa ukku a fahimtata:
.
1). Kyakykyawar Niyya: amma da karancin Ilimi ko rashinsa, kila saboda kishinsa ga addiniSa, da kokarin bawa Addini kariya da wadanda sukayi dakonsa da ba shi kariya! Sai dai hakan bazai zama Uzuri gareshi ba, tunda Shari'a ta wajabta mashi neman Ilimi, da tambaya akan abunda bai sani ba!
.
2). Ta'asubanci (Taqalidancin-Bisa saon rai), Kiri-Kiri ga gaskia amma don ta sabawa mazhabarka saika ajeta ka dauki watanta, Ita kuwa gaskia:
"Ana daukarta ne, koda ta fito daga kafirin da yafi Fir'auna da hamana kafurci, Matukar dai ta cancanci ta zama gaskia".
.
3). Son Shuhra: Kutsa kai cikin abunda baka da ido acikinsa, don kawai son shuhra, zaka gansu sai yawan jayayya, amma ba dalili na shari'a, idan kuma ya kawo dalili sai kaga bashi da alaqa da maudu'in.
.
Abun mamaki:
"Idan mutum bai san abu ba, to kuwa shi yana ganin tayaya za'ayi wane ya sanshi, ko kuma riko da fahimtarsa kota malaminsa a matsayin fahimtar shari'a, ya watsar da duk wata mahimta ta magaba don kawai kare mazhabinsa"
.
Wani ma:
"Har sahabbi zai iya cin mutuncinsa matukar dai kimar mazhabarsa zata wanzu, Ibnul Arabiy yana cewa: tur da fahimtar da sai anci mutumcin sahabi"
.
Yana daga cikin babbar Matsalar da Muke Fuskanta shine, Rashin Fahimtar mas'aloli na shari'a, wanda yake da matukar muhimmanci ka fahimcesu kafin ka tsoma baki akai, amma saboda wani Kulli dake zuciyar mutum sai ya aukawa mai gaskia yayi masa inkari bisa zalunci.
.
(Zan Cigaba)
Ibrahim Yunusa Abu-ammar
11/04/1439H - 30/12/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter