Subscribe Our Channel

Tabbas Maulidi Bid'a ne //4
.
- Shin Ana Lura da aikin Sahabbai domin ganewa ko tabbatar da Ibada?
.
Wannan Tambaya Malam Salis G. Amin ya tattaketa don haka mai neman karin bayani sai yayi duba izuwa timeline donsa! Walahul Musta'aan.
.
Abunda ya kamata mu dan leqa shine, su masu kokarin sokewa da aibata sahabban manzon Allah dasu da masu goyan bayansu tuni suka nuna cewa Imamansu da waliyyansu sune majibinta addini saba musu sabama Allah da manzonsa ne, kai yanama jawo bala'i da fitina a doron kasa.
.
Acikin Kungiyar bata, watau shi'a a kwai wata firqa mai suna Al-Albaa'iyyah, su wadannan firka wani daga cikin mawakinsu yana waka yana cewa:
.
"Tawalliitu Ba'adallahu Fid deeni kamsatu - Nabiyyan, Wa Sibdaiihi, Wa Shaikan, Wa Fadima" Intaha. Ma'ana: "Majibinta Bayan Allah a cikin wannan Addini Mutum biyarne, Annabi AS, da Jikokinsa (Hasan da Husaini) da Wani Mutum (Aliyu) da Fadima (Diyar Annabi).
.
- Haka zalika Muhammad Mazandaraniy a cikin Littafinsa Sharhu Usulul Kafiy (2/225) Yana cewa: "Lallai Hadisan Kowanne daya daga cikinsu (Watau Imamai) Tsarkaka to maganar Allah mai girmace (Maganar tasu)
.
Shima Khumaini a cikin Littafinsa Al-Kafiy, A Usulu (1/191-192) Ya Bude babi Na Musamman Mai Suna "Babin Da Zaiyi Magana akan Jibintar Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah Da Iyalansa, da Imamai Amincin Allah a garesu, a cikin Al-amarin Addini" a cikin Wannan Ya Ambaci Hadisai Goma.
.
Mai Littafin Basa'irud darajatil Kubra fi Fada'ili Ali Muhammad Salawatul lahi Alaihim Ajma'in Yana cewa a (1/138), (Babin Mai magana Akan Imamai, kuma Lallai Hujjar Allah ne su...) Ya kawo wata ruwaya cewa Lallai Imamai sune "Taskar Allah, Ma'abota Addinin Allah, kuma akanmu aka saukar da Littafin Allah, Ta Dalilinmu ake bautawa Allah, ba donmu ba da ba'a san Allah ba"
.
Dama kuma suna cewa, Wai Sayyidina Aliyu yace: "Wannan Littafin Allah ne kurma (Kur'ani), Nine Littafin Allah mai magana" Duba: Al-Fusulul Muhimmad Fi Usulul A'imma (1/595) Dama Kuma sunce Wai An Tambayi Abi Ja'afar Muhammad Bin Aliyu Imami na Biyar kenan, Wai ance dashi: "Kur'ani Zai iya isarsu? Sai yace Eh in kun samu tafsirisa, sai akace dashi: wanene Manzon Allah SAW ya fassara mawa, sai yace: Eh, Ya fassarawa wani Mutum guda daya, Kuma ya bayyanawa Al-Umma sha'anin Wannan Mutumin, Shi wannan Mutumin Shine Aliyu Bn Abi Dalib" da Wannanne ma aka aka kirashi da Littafin Allah mai magana Duba: Al-Kafiy Cikin Usul (1/179) Babi acikin Sha'anin Innaa Anzalnaahu fii Lailatil Qadri da Tafsirinta...
.
A Nan sai Muce Yan Shi'a kalubale gareku, ku kawo mana Tafsirin Imam Ali akan Ayar Nan ta suratu Yunus ayata 58, ??, sannan su fada mana yaushe Sayyidi Ali yayi maulidi, da kuma fatawarsa kansa
.
- Suna cewa ManzonCin Annabi Muhammad Baya cika sai da koyarwar Imamai Ku duba wannan akida a littafinsu Mai suna Sha'a'iril Husainiyya Shafina (13-14) na Hasan Shiiraaziiy, da Al-Kafi, a usul (1/270), da biharul Anwar (28/26)
.
Haka suma Sufaye su nasuma abune sannanne domin malamansu sunsha ikrari a wurare da dama a wannan kasar cewa bala'i zai auko idan ana sabawa waliyyansu, wannan basa bukatar wani dogon bayani Amma:
- Shehu Tijjani Yayiwa Annabi karya da fadin falalar yi masa da'a, kamar yadda yazo a cikin Jawahirul-Ma'ani (1/130-131), Haka da Irin Yadda yake fadin Falalar Binsa da kuma sauran waliyyai da Kaunarsu Wannan yazone a cikin Littafin Jawahirul-Ma'ani shima a (2/176), da kuma Arrimaah (2/405-413) da sauransu!
.
Wannan Tattare da cewa wadannan basuga Annabiba basuyi rayuwa dashi ba, babu wata Alaka da take da manzon Allah da su data wuce addini, sukuwa sahabbai duk sun samu wannan bugu da kari sune manzon Allah yace masu: "Ku isar mani (da sakona) koda da aya dayace" Allah ya kara yarda dasu Ameen.
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
01/4/1439H - 19/12/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter