HADUWA A KAN BIN QUR'ANI DA SUNNA SHI NE TAFARKIN SHIRIYA
.
Shaikhul Islami ya ce:
وأما دين الله وهداه الذي أنزل به كتابه وبعث به رسوله فهو اتباع كتابه وسنته في جميع الأمور وترك اتباع ما يخالف ذلك في جميع الأمور والإجماع على ذلك
الاستقامة (1/ 270)
.
"Amma Addinin Allah da shiriyarsa da ya saukar da Littafinsa da shi ya aiko Manzonsa da shi shi ne Bin Littafinsa da Sunnar Manzonsa a dukkan lamura da barin bin dukkan abin da ya saba musu a dukkan lamura, da kuma haduwa a kan haka".
.
Wannan shi ne abin da Ayar nan take nuni gare shi, wato fadin Allah Madaukaki:
{وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا } [آل عمران: 103]
.
Sai Allah ya yi umurni da haduwa a kan Igiyarsa wacce ta kunshi abin da ya aiko Manzonsa da shi na Qur'ani da Sunna, kuma ya yi hani a kan rarrabuwa a cikinsa.
Dr. Aliyu Muh'd Sani
Home
»
masha Allah
» HADUWA A KAN BIN QUR'ANI DA SUNNA SHI NE TAFARKIN SHIRIYA - Dr. Aliyu Muh'd Sani