Subscribe Our Channel

Mut'a /5
.
Hakika Hadisi Ya Inganta daga Jabir dan Abdullahi Lallai Yana Cewa: "Mun Kasance Muna Yin Mut'a Damtse Na Dabino, da Gari, na wasu yan kwanaki, Alokacin Manzon Allah, da Zamanin Abubakar, Har sai da Umar Ya Hanamu Yin Shi, A cikin Sha'anin Amru bn Harith" Duba: Muslum (1405), da Abu-Dawood (2110).
.
- Wannan Kuma kamar Yadda Malamai Suke bayani cewa: "Wadanda Suka aikata Mut'a a lokacin Manzon Allah da Abubakar da Umar, Hanin Mut'ar da Soke shi bai Isa garesu ba" Duba: Mugni: (6/644), da Fiqhus Sunnah Lin-Nisa' : (376).
.
- Wannan Sha'ani Kuma a bayyane yake, Kamar Yadda Hukuncin abunda Annabawa suka bari ya boyu ga Nana Fadima, Wanda Imamul-Bukhari Ya Ruwaito Ruwayar Manzon Allah SAW Yake Cewa : "Ba'a Gadonmu mu Annabawa, Abunda Muka bari Sadaka ne".
.
- Haka Zalika a wurare da dama wani hukuncin Ya Boyu wurin Wasu Sahabban Sun halatta ko sun haramta wani abun akan abunda suka sani, Kamar Abu-Hanifa Ya Karhanta Sallar Rokon Ruwa Saboda Bai Samu Hujja daga Manzon Allah ba, Amma daga baya bayan Dalibansa Hujja ta riskesu, sun yiwa malaminsu addu'a ta gafara, kamar Maliku daya karhanta Azumin tasu'a, da sauransu. Allah ya taimakemu
.
* Haka Kuma Ya Tabba daga Ibn Abbas Shi yana ganin Yin Auren Mut'a, Amma fa sai da lalura, Daga Abi-Jamrah Yace: Naji Ibn Abbas An tambaye Shi kan Mut'a sai ya saukaka (Ya Halatta), Sai Maulansa Yace: Shin Wannan a lokacin Tsanani da kuma karancin Mata? Sai Ibn Abbas yace "Eh!" Duba: Bukhari (5116), Dahawiy: (3/26), Baihakiy (7/204).
.
- Wannan Shima a bayyane yake kamar na farko, Sannan kuma Mu sani Ibn Abbas, Ahlul-Baiti ne, sahabi, Babban Malamin Sunnah, Babban Malamin Hadisi, Kuma abun dogaro ne a Muslunci, Matukar Bai Sabama manzon Allah ba, Allah ya kara yarda dashi, a Wannan Mas'alar Sahabbai da mada sun saba masa, kuma a karshe ma shima ya janye wannan ra'ayin kamar yadda mukayi bayani a baya, a Duba: Al-Mabsuud (5/143) domin karin bayani.
.
Sannan Sha'anin A yar nan ta Cikin Suratul Ma'ida Ayata (24), Malamai Sunyi Sabani akan Ma'anar da Gabar Ayar ke nufi, Wani bangare sunce Mut'a, Amma Jamhurin Malamai Sun tafi akan aure ake nufi, kamar Yadda dai Ibn Kasir a cikin Tafsirinsa Mujalladi na (1), karkashin tafsirin ayata ta (24), yayi bayani, haka Imamul khurdubi Mujalladi Na Biyu, da Ibn Jarir Mujalladi na Hudu.
.
- To koma dai Mut'ar ce idan ka koma wadancen tafsiran bayan Sun kawo maka tafsirin ayar da sabanin da aka samu, sai kuma su rufe da Sokewa da haramcin Mut'a, kamar Yadda idan ka karanta zaka gani, kamar yadda dai Munsan Ilmun Nasikhu Wal Mansukh.. Kamar Yadda Allah ya fada a suratul bakara (102), da wasu Ayoyin... Musun Haka kuma Dabi'ace ta kafuran farko kuma kafurci ne..
.
.......!
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
04/02/1439H - 23/10/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter