Don Sun Zagi Saudiyya ba Abin Mamaki Bane.
.
BawaI Suna Cin Zarafin Saudiyya bane Kwai Da Yimata Kazafi don Wata Manufa da mu muke tunani ba, da kiyayya ga Saudiyya, sai don Rufin Asirinsu, da Kuma Kashin MiyarSu da suke karewa, domin kuwa Lallai Gaskia ce zata Bayyana, idan Shirin saudiyya ya bayyana.
- Bari Mu Aro Salon Babban Malamin Sunnah Ibn Taimiyya: "Da Zamu Kaddara cewa abinda Saudiyya Zatayiwa Hadisan Manzon Allah Mai Tsira da Amincin Allah Shine Abunda Suke Riyasa Sai Muce, To ai ku kunfi Saudiyya Sharri, Domin Ku Zindir Kuka yiwa Muslunci, Tun daga Annabin Har Zuwa Al-Qur'ani da Sunnah, Ku Sufaye: Kun Girmama Shehunnan ku da Waliyyanku akan Allah da Manzonsa, Kun Girmama Littattafanku da maganganun Shehunnanku akan, Littafin Allah da manzonsa, Shi'awa kuma Sunfi Haka Sharri da Barna, Yan Boko Akida Bama Sanin Addini ba, bama addinin Bane Gabanku Sai Iskanci da yahudanci, Bakaken Yahudawa kenan"
.
- A Cikin Jawarihil Ma'ani: Sheikh Tijjani Yana Cewa: "Ya Tambayi manzon Allah akan Wanda ya bishi kuma ya karbi sakonsa, shin za'a yafe masa zunubansa kuma a shigar dashi Aljanna bada hisabi ba, kuma su kasance dashi a Illiyyin, sai manzon Allah ya Amsa masa Injishi" ku duba: Jawarihil Ma'ani (1/130)
.
"Ya Tambayi Allah Falalar Siyyidina Rasulullah, da kuma Shigar da duk wanda ya bishi ba tare da hisabi ba Al-janna, da kuma Iyayensa da kakanninsa..." Duha Jawarihil Ma'ani (1/130-131)
.
- Wanda Ya zage Tijjani Kafurine dan Wuta Duba: AR-Rimaah (2/49), Wani Bugun (2/426) sai Kace Wani Annabi, Kuma yace Shine Cika-Makon Waliyyai, Sugaban Masana, Sugaban Suddikai, Wasidar Bayi da Mahaliccinsu, Duba AR-Rimah (2/4), wata Nuskar (1/398).
.
Kai Shi Allahma Yake Gani Kuru-Kuru, Duba Jawarihil Ma'ani: (1/160), Haka kuma Allah yana yin Huluyyi (Ma'ana Yana Narkewa cikinsa, Sai kace wani Al-Janni) Ku duba Jawarihil Ma'ani: (2/5), wata nuskar (1/126) Kai Yanama Iddi'a'in don kayiwa wani Bauta to Allah ne kayima wa ba kowa ba (Akidar komai Allah ne) Duba: Jawarihil Ma'ani: (1/219), Wata Nuskhar: (1/184-185), Kadan kenan..
.
- Ku karanta DabakatuL Auliya'a kuga Shegantaka Iri-Iri.
.
Yan Shi'a kuwa ba'a magana, don su a akidarsu Sakonma Ba wanda yakamata akaimawa bane aka kaimawa, Mala'ika jibrilu yayi rafkanuwa: Ku Duba: Nurul-Burhani (2/310) Wannan ne yasa suke cewa Littafin Allah Kurma (Kur'ani) da Littafin Allah mai Magana (Aliyu) Duba: Fusuulul Muhimmah (1/595), Wasa'ilis Shi'a (18/323) Kunga tun nan bama sai Munje da Nisa ba, Ance ka kawa wane ka kaiwa wane kuma acikin Sha'anin Addini? Tam Malaman Jarhu ko tsaf zamu Jarha mai rin wannan hali, aki karbar hadisinsa ba Al-Kur'ani bama.
.
Kuma dama can Su yan Shi'a Sun zargi sahabbai da canza Al-Kur'ani, da soke soke cikinsa Duba: AsalusH Shi'a Wa Usuluha (81), Bayan Sune mafifita Wannan Al-Umma, To don Sun Zargi Saudiyya wannan ai ba abin mamaki bane.
.
- Su kuwa Wadancen Yan bokon Menene na mamaki akansu bayan Renon Yahudawa ne, Malaman Taribiyya na cewa: "Yadda mai tarbiyya ya kasance haka wanda aka tarbiyyantar zai kasance", Mu karanta Al-Kur'ani Muga Tsiyar Ya Hudawa marasa kunya da Tarbiyya.
Allah ya sauke
.
"To Amma fa Kaddarawarcen Ba zata samu matsugunni ba, domin kuwa saudiyya Al-herine zata assasa, Kuma Muna Addu'a Allah ya taimaketa, yayi mata jagorancin na Al-Heri"
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
05/02/1439 24/10/2017