Akidar Jahmiyya ce da Mu'atazilah, da kuma Masu kwashe-Kwashe Wato Shi'ah Cewa:
"Al-Qur'ani Halittar Allah ne, ba Maganarsa ba" Malamin Shi'a Majlisi Acikin Littafinsa Biharul Anwar: (89/117), Ya Kulla babi na Musamman Mai Suna "Babu Annal Qur'ana Makhluuqun" A ciki ya ambaci Ruwayoyi (11), Haka babban Malamin Shi'a Muhsin Ameen yana cewa: "Shi'awa da Mu'atazila Suna cewa: Al-Qur'ani Halitta ne" Duba: A'ayanuSh Shi'a (1/154).
.
Lallai Wannan Akida, Akidace Batacciya, Akidace Ta kafurci wacce ke warwama mutun imaninsa, Sannan Wannan ba' akidar Ahlus-Sunnah (Manzon Allah da Sahabbai da Tabi'ai da Mabiyansu) bace, An Tambayi Imamur Ridah (Allah Yayi masa rahma): Akan Al-Qur'ani (Me zakace)? Sai Yace: "Lallai Shi Maganar Allahce ba Halitta ba" Duba: Tafsirin Iyashiy: (1/17) Babi Mai Magana akan Falalar Al-Kur'ani.
.
Tambihi: Ubangija Ta'ala Shine Ya Haliccemu kuma Ya Halitta ayyukanMu (Da Aalam baki daya), Kamar Yadda yake fada a Suratus Saffat (96), Sannan Ya Sanyamu Masuyin Daidai da Kuskure domin ya Jaraba ImaninMu, MaganarMu da Mukeyi ta yau da Kullu Halittar Allahce don haka Kasantuwar Asalin Fidirar Halittarmu Masu kuskurene masu yin daidai a cikin kalamanmu, Wannan shine Yasa Mu'atazilawa shi'awa da Jahmiyya da Mabiyansu suke jifan Al-Kur'ni da Halitta, dacewa wai ba maganar Allah ba ne, domin su kuskurantar dashi su samu damar kutso da akidunsu cikin Addini don su bata addini.
.
Allah Ya Tsare Mana Imanin Mu, daga Fadawa Halakar Halakakku.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
29/01/1439 - 19/10/2017
Home
»
Bayyana Gaskia
» Akidar Jahmiyya ce da Mu'atazilah, da kuma Masu kwashe-Kwashe Wato Shi'ah Cewa