Aslm malam inada tambaya na kasance na taba zuwa wajen matar mahaifina munaso mu aikata sabon ALLAH nida ita,amma bamuyi ba yanzu haka shekararta 3 da rasuwa a lokacin ina ganiyar
sha'awa,malam menene hukuncin mu pls a boye sunana?
.
Amsa
****
Waalaikumus Salam Dan Uwa, Lallai zina ta cikin manya-manyan Laifuka da mubangiji ta'ala ya hana kusantarsu, kamar yadda yake fada acikin suratul Isra'i ayata 32 "Kuma kada ku kusanci zina, Lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya" Haka kuam kuma Yake cewa: "....kuma kada ku kusanci abubuwan Alfasha abin da ya bayyana daga gare ta, da abin da ya boyu...." [An'am: 151], Imamud dabari a cikin tafsirin sa a karkashin tafsirin wannan ayar ya ruwaito wani asari daga ibn Abbas da sanadi hasan, Ibn Abbas yana cewa: "mutanen jahiliyya Su kan zargi zina idan anyita a bayyane amma idan an yita a boye babu laifi", sai Ubangiji ta'ala yace:gaba daya da bayyanen da boyen duk haramun ne.
.
Imamuz Zahabi a cikin Littafinsa Al-Kaba'ir ya kawo zina a dabaka ta 12 daga cikin manya-manyan kaba'ira daya jero, da kuma hadisai da ayoyi da yakawo akarkashi.
.
— Don haka dai dan uwa kusantar zina yana daga cikin manyan zunubai, shiyasa Allah yayi hani akan hakan kamar yadda ya bagata, sannan manzon Allah ya tsawatar ta hanyar:
— Hana kebanta da mata
— Hanasu Shigar da bata dace ba.
— Daga sautin su.
— Fitar Jahiliyya
— Hanasu tafiya su kadai
— Hanasu fesa turare idan zasu fita.— Hani akan hada yara mace da namiji a shimfida guda daya.
— Da duk wata hanya da zata kai ga zina.
.
— Don haka dai yakai dan uwa hakika kayi Laifi Don haka wajibine agareka ka tuba, tare da nadama da kuma Al-kawarin bazaka komama wannan laifin ba kamar yadda Imamun nawayi ya bayyana acikin littafinsa Riyadus-salihin BABUT TAUBAH, sannan ka biya da Istigfari da lizimtar ayyukan kwarai, da nisantar duk abunda zai kaika ga sabama Allah
Wallahu A'alam.
Domin karin bayani Duba: [Saheehu Fiqhus-Sunnah Juz'i na biyu shafi na 19-41], da [Tayas-Sirul Allam Mujalladi na 3, Juz'i na biyar shafi na 597], [Riyadus-Salihin Babin Tuba].