Taba ka Lashe //3
.
Hakika Uwar Muminai Khadija Yar Khuwailid, Allah ya kara yarda da ita, ta kasance ga manzon Allah Mata ta farko a tarihin Rayuwarsa, Kuma Mata ta gari abun soyuwarsa, Wacce ta fito daga babban gida kuma ma'abociyar dukiya da Matsayi a garin Makka, Ta kasance Mai so da kaunar Manzon Allah, ta tarairayi Manzon Allah da kula dashi wanda baya misaltuwa, ta taimaka mashi da dukiyarta da karfinta, da matsayinta, Shiya aka samu a wurare da dama Allah da ManzonSa Mai tsira da AminciSa suna yabonta da kuma labarta mana irin matsayinta da sakamakonta Duniya da Lahira. Duba: Ahmad (1/263), (3/135), Muslum (75), Al-Hakim (2/593), (3/157), Turmizi (3878).
.
* MAI-MAITA GININ KA'ABA
- Lallai Ginin Farko da aka fara ginawa a wannan duniyar domin Ibada Shine dakin ka'aba, sannan Masjidul Aqsaa, ya kasance tsakaninsu shekara Arba'inne, kamar yadda yazo a hadisin Abu Zar, Sannan ayar nan ta cikin suratu Ali'imran (96), bawai tana nufin babu wani gini da aka tabayi a duniya kafinsa ba, A'a ginin farko da aka gina don Ibada a tarihin duniya shine Ka'aba, kamar yadda Imamul bukari ya ruwaito: (6/469), Sannan kuma Ibn Hajar a cikin Fathul bari: (6/470) ya karfafeshi da Ruwayar Ibn Abi Hatim.
.
- Malamai Sunyi Sabani akan Wanda Shine farkon Wanda ya fara gina dakin ka'aba: Wasu sukace, Mala'ikune farko, wasu sukace A'a Annabi Adam ne, wasu suka ce A'a Annabi Ibrahim da Isma'il ne, Amincin Allah ya kara tabbata a garesu baki daya.
.
- Amma Magana mafi Inganci itace Dakin ka'aba ya kasance ne tun kafin Annabi Ibrahim, Sai dai kawai yanayi na tsawon zamani yasa ya rushe amma kuma Alamarsa na nan (foundation), Shi annabi Ibrahim Da Isma'il AS, Sun Sake ginin ne kamar yadda Allah ya bada labarin hakan a suratul bakara (127)
.
- Yayin da Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah Yakai Shekara Talatin da Biyar, Kuraishawa sun nufaci sake ginin Ka'aba, inda suka shata sharadin bada gudunmuwar Wannan aiki ya kasance dukiya ce ta halal, hakan yasa aka samu karancin gudunmawa saboda kasancewa yawancin sana'o'insu na maguzancine, Hakan Yasa gudunmawar da aka tara ta kasa isa a gina ka'aba a asalin asasin da Annabi Ibrahim ya assasata dashi da dansa Isma'il (A.S).
.
- Annabi yayi musharaka dasu wajen wannan aiki, wanda saboda Yarda dashi da Amincewarsu a gareshi ya sanya suka sanyaShi a matsayin Al-Kali akan dora Hajrul aswad, Yayin da suka samu sabani akan wanda ya cancanta ya dora wannan dutse, Wanda kuma Annabi Mai tsira da Amincin Allah, yayi hukunci na hikima wanda ya dadadan ran kuraishawa, Abun da kuwa ya faru shine, Manzon Allah ya shinfida gautansa ya dora Bakin dutsen akai, sannan ya umurcesu da su turo wakili daga kowacce Kabila domin su kama wannan bargon shi kuma ya sanya hannunsa mai Al-barka ya ida dora dutsen inda yake. Duba: Sahihul Bukhari: (364), (3/513), Muslum: (340), Dabarani da Ahmad Duba Majmu'u na haithami: (3/689), Fathur Rabbaniy: (20/198-199), Arrahiqil Makhtum: (59).
.
ALAMOMIN ANNABTA..
- Yayin da Manzon Allah yakai Shekara 40 da haihuwa sai Al-momin Annabta suka fara bayyana a gareshi, yayin da ya zabi kebewa daga mutane a cikin wani kogon dutse ana cewa dashi Hira, wanda daga garin Makka zuwa Hira Mil 6ne ko wanin hakan, Manzon Allah ya kebene a kogon hira yana nazarce nazarcen rayuwa da haluttun Allah da kuma sakunnan Annabawan da suka gabata, wasu kuma sukace yana ibada ne akan Addinin Annabi Ibrahim, bayan nan manzon Allah yakanyi wasu mafarkai da sukasha babanban da mafarkan sauran Mutane wanda ke nuni akan Kusantowar Annabta, Sannan kuma ya kasance duk mafarkin da yayi SAW yakan tabbata, ya kuma wakana kamar yadda yayi mafarki, kamar dama ba mafarkin bane yayi. Duba: Fiqhur-Sira (98, 99) Na Gazali.
.
AN FARA SAUKAR DA WAHYI.
(Akwai Cigaba)
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
26/12/1438H. 2017M.