Taba Ka Lashe //2
.
AUREN KHADIJA DA ANNABI
* Hakika Allah Ta'ala ya Kare Annabinsa Mai Tsira da Amincin Allah, daga Munanan Halayen Jahiliyya da Dabi'u marasa kyawu, domin ya kasance dukkanin Rayuwarsa ta Tsarkaka, tarihin rayuwar sa ya kasance fari kal, babu wata masoka a cikin shi. Abu-Na'im cikin Dala'il: (127), Musnad Ahmad: (4/222), Haisamiy: Majmu'u (8/225).
.
Kyawun Halin Manzon Allah, Gaskiar da Amanarsa da Dabi'unsa Kyawawa, da kuma abunda ya bayyana gareta ko aka bata Labari, da abunda yaronta maisara ya labarta mata na karamar ma'aiki, ya sanya zuciyar Uwar Muminai Khadija Yar Khuwailid Al-Asadiyy So da kaunar Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah.
.
Ita dai khadija ta kasance daya daga cikin dangi mafi girma da daukaka a cikin kuraishawa Banu Asd, acikin garin makka, kuma ta kasance daya daga cikin mata yan kasuwa masu kudi a wannan lokaci.
.
Ibn Ishaaq Yana cewa: "Khadija 'Yar Khuwailid ta kasance Attajirar Mace, kuma ma'abociyar daukaka, Wasu mazaje (Yan Kasuwa) Sukan fita fatauci da dukiyarsa, Akan abunda take sanya Musu (Na Lada), kuraishawa kuwa sun kasance Mutanene Yan Kasuwa.
.
Yayin da Khadija ta samu Labarin Manzon Allah Mai tsira da Aminci Allah, na abunda aka labarta mata na gaskiarsa, da girman rikon Amanarsa, da kyawawan Halayansa.
.
Sai ta Aika masa, Ta bukaci daya fita fatauchi da dukiyarta zuwa sham, ta bashi dukiya wacce bata taba ba waninsa ba, daga cikin masu fatauci da dukiyarta, ta hadashi da yaronta, ana cewa dashi maisara, sai manzon Allah ya karbama bukatarta, ya fita da dukiyarta (Wannan fataunci), tare da yaronta maisara har suka isa sham.
.
(Acikin wannan tafia tasu: Manzon Allah da Maisara) Sai Manzon Allah Ya sauka a karkashin Inuwar wata Itaciya kusa da bukkar wani malami daga cikin malaman mishin, sai Wannan malami (Wanda wasu malaman suna cewa bahira ne wanda ya sa aka maida Annabi gida yana yaro, lokacin da Amminsa zai fita dashi fatauci) yace da Maisara, wane mutumine wannan ya sauka karkashin wannan itaciya sai yace: Wani mutumne daga kuraishawa daga cikin mutanen harami, sai malamin yace babu mai sauka karkashin wannan itaciyar sai Annabi. Duba: Fiqhus Sira (84-85).
.
Cikin Wannan tafia Maisara yaga karamomi daga manzon Allah kamar inuwar girgije ga Annabi In rana tayi zafi, wata ruwayar kuma Mala'iku ne guda biyu ke masu Inuwa, yayin da maisara ya isa gida saiya labartawa khadija abunda Malamin nan ya fada masa, da kuma irin karamomin daya gani tare da Manzon Allah. Dabakat na Ibn Sa'ad (1/129) da Ibn Hisham (1/165-166)
.
Hakan Yasa khadija ta aika Qawarta Nafeesah, zuwaga Annabi bayan sun binciki nasabarsa, domin ta gabatar da bukatar kawarta ga Annabi, hakan kuwa akai bayan ta sameshi sun tattauna, ta gabatar da Qawarta ga Annabi ta wani salo da kuma hanyar data dace, shi kuwa Annabi ya karba mata.
.
Ita kuwa Nafeesa sai taje ta shaidawa kawarta Yadda sukayi da Annabi - Soyayya dai ta kullu - sai Abu- Dalib da Hamza Ammomin Manzon Allah Suka tafi zuwa ga Ammin khadija, Amru dan Asd, suka tattauna dashi akan Auren khadija da Annabi, aka sanya sadaki.
.
- Amr Dan Asd ya aurar da khadija ga Annabi, A Wannan Wurine Abu dalib ya tashi ya danyi jawabi, dangane da Family dinsu da irin darajar gidansu, Acikin Jawabinsa yake cewa: "Lallai dan dan dan-Uwa na wannan (Muhammad Dan Abdullahi) baza a hadashi da wani mutum ba face yayi fice akansa wurin kyawun halinsa da falalarsa, da daukakarsa, da hankalinsa, da girmansa da kaifin basirasa. Siratul Halbiyy (1/226)
.
- Bayan Wannan aure mai cike da Al-barka da Al-herin Allah khadija ta samu labarin aurenta da Annabi haka yasanyata farin ciki sosai hardai ta hada wata kwarya kwaryar walima don murnar wannan al-Amari daya faru, ta hada abinci da abun sha ta gayyaci jama'a, da wasu jama'a daga kuraishawa akaci aka sha. Musnad Ahmad (1/312), Baihaqi (2/73) Dabarani (12838), Haithamiy (9/220).
.
(Akwai Cigaba)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
20/12/1438H