Subscribe Our Channel

Taba ka Lashe //1
.
Hakika Allah Jalla wa Ala, Ya Zabi Manzon Allah A Matsayin Sugaban Annabawa, sannan Mafi Al-Khairin Halittun Allah, kuma a matsayin Dan Aikensa zuwa ga duniya baki daya Amincin Allah Ya Kara tabbata a gare Shi Zababbe daga Cikin Zababbu, Sannan Kuma ya zaba masa, Iyalai Mafi Kyawun Iyalai: (Matansa da Yayansa Da Danginsa), sannan ya zaba masa Mataimaka Mafi kyawun Hali da Juriya da sadaukarwa Yardar Allah ta kara tabbata a garesu baki daya.
.
Hakika Manzon Allah ya fito daga wani tsatso mai girman daraja watau tsatson Annabi Ibrahim, kamar yadda Imamul Bukari yake fada: "Shine Abul-Kasim Muhammad Dan Abdullahi Dan Abdul-Mudallib Dan Hashim ..Har zuwa.. Ma'ad Dan Adnaan" Duba: Sahihul Bukhari (3851).
.
Hakika Ubangija ta'ala Yayi masa zabi tun daga tsatsonsa har kabilarsa Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah Yana cewa: "Lallai Allah Mai girma da Daukaka Ya zaba daga Yayan Ibrahim, Isma'il, Sannan Ya Zaba daga Banu Kinanah, Kuraish, Sannan Ya zaba daga Kuraish, Banu Hashim, sannan Ya Zabeni daga Banu Hashi" Duba: Muslum (2776) Kuama Allah Ta'ala ya zabeShi A matsayin Shugaban 'Yan Adan A Ranar Al-kiyama. Duba: Musnad Imamu Ahmad (11000), da Darihi (52).
.
An Haifi Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah A Ranar Litinin Sha biyu(12) ga Wata Rabi'u Auwal Shekarar Giwaye (Duk da dai akwai sabani mai girma wurin tahdidin ranar da Aka haife shi) Sahabi Abdullahi Dan Abbas da Jabir Al-Ansariy Allah ya kara yarda dasu, Sunce: "An Haifi Manzon Allah Mai tsaira da Amincin Allah A Shekarar Giwaye Sha Biyu (12), Ga watan Rabi'u Auwal, Cikinta ne akai mi'iraji dashi zuwa sama, cikin tane yayi Hijira, Cikinta ne ya rasu" Wannan Shine Wanda yafi Shahara A wurin Malamai, Allah shine mafi Sani Duba: Musannaf na Ibn Abi Shaiba (1/119).
.
Allah Ya Girmama dukkanin Yan Adam da haihuwar Shugabansau, Ya Haskaka duniya daga duhun da take ciki da haihuwarsa Kamar Yadda yake fada SAW: "Nine Addu'ar Annabi Ibrahin, Nine Busharar Annabi Isah, Nine Hasken da Mahaifiyata tagani ya fito daga gareta ya haske Ganuwar Sham" Amincin Allah Ya Kara tabbata a gare Shi.
.
Manzon Allah Yazo duniya yana maraya ta gefen Uba, yayin da yakai shekara Shidda sai ya zama marayan Uwa da Uba, Mahaifinsa ya rasu yana cikin mahaifiyarsa, Mahaifiyarsa kuma ta rasu yana dan Shekara Shidda, yayin da kakansa Abdul-Mudallib ya rikeshi tsawon shekara biyu, shima yace ga garinku nan, sai ya koma hannun kakansa Abu Dalib.
.
Manzon Allah ya taso cikin Maraici, da kular Amminsa yayin da ya rike shi tamkar da. Ya rayu cikin da'a da kunya, da kyawawan Halaye, ya kasancen Amintacce, kuma yardajje, abun yabo a wurin mutanen makka da kewayanta.
.
Ya kasance Sana'arsa Itace Kiwo ga Ahlin Makka, Duba: Sahihul bukhari (3/516) hadisi na (2262), Muslum (1/5-6), Sannan fatauci Fitarsa na farko da Amminsa Abi-Dalib wanda bai samu isaba sakamakon Labarin da Rahib Bahira Ya bada na Alamun Manzancinsa, da hatsarin shigarsa sham Duba: Turmizi 3/296), As-Sirah Na Gazaliy: (79), Fitarsa tabiyu itace Fataucin da yayiwa sayyada khadija Duba: Fiqhus Sira (84-85)
.
(Zan Cigaba)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
18/10/1348H
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter