Meya Faru a Ghadir //1
.
A cikin Wannan Dan Takaitaccen Bayani zan hakaito wata yar tattaunawa da akai tsakanin Sunnah da Shi'a dan ganeda abunda ya faru a Ghadir, a takaice, tare da kuma tambihi.
.
Ga Tattaunawar kamar haka:
- Bayan wata yar gajeriyar tattaunawa da sunnah da Shi'a suka gabatar dan gane da abunda ya shafi Imama a tarihin Muslunci da matsayinsa a addinance sai Shugaban Yan Shi'ar Yace da Malamain Sunnah yayin da yakeso ya bayyana masa dalilin shi'a akan imamancin Sayyiduna Ali:
.
* Shi'a: — "Dalili na farko (Abunda ya faru a Ghadir Kum), Wannan hadisi Sanannene a wurinku (Mu Ahlus-sunnah yake nufi), kuma acikin Littafinku abun dogaronku, kuma wannan daliline kwakkwara, isashshe, tabbatacce akan Imamancin Imam Aliy Aminci Allah a gareshi"
.
* Sunnah — "Ya kamata ka bijiro dashi (Hadisin), Sai dai Ina neman a bani dama Inyi ta'aliqi akanshi, har gaskia ta bayyana Mai rabauta ya rabauta da Bayyanarta, Mai halaka ya halaka daga bayyanarta"
.
- Ma'ana Malam Yana nufi: Mai rabon Shiryuwa daga gareku ya shiryu da bayyanar Wannan Gaskia wanda kuma baida rabo yanzu, sai batansa ya rinjaye shi ya kara bacewa.
.
* Shi'a — "Yayin da Manzon Allah ya Kama hanyar madina bayan ya gama hajjin bankwana, a shekara ta 18 a wata zul-Hajji Sai ayar nan ta sauka akansa: "Yakai Kai Manzo, ka Iyar da Abinda aka saukar zuwa gare ka daga ubangijinka. Kuma idan baka aikata ba to ba ka iyar da manzancinsa ba ke nan. kuma Allah yana tsare ka daga mutane Lallai ne, Allah baya shiryar da mutane kafurai" Suratul Ma'ida: (67)
.
- Sai manzon Allah ya yada zango a Ghadir kum a juhfa - Wurine tsakanin Makka da madina - ya tsaya nan har sai da wadanda ke bayansa suka hadu dashi, wanda suka wuce shi kuma suka dawo, Sannan ya kira (mutane) Sallar Jam'i, sannan yayi sallar Azahar (Da mutane) sannan ya mike yayi khuduba ga mutane, Ya kasance acikin kudubar tasa lallai shi yana cewa: (Shin Yanzu baku san cewa Nine Mafi soyuwa ga dukkan muminai akan kawunansu ba (sama mumini yaso wani ba ni ba), sai suka ce hakane ya Ma'aikin Allah, sai yace, Shin Yanzu baku "Sani" ko "Shaidawa" cewa nine mafi soyuwa ga mumini akan kansa ba (Ya Soni Sama da yaso kansa), sai sukace haka ne ya ma'aikin Allah, Sannan sai ya kama hannu Aliyu Dan Abi dalib ya daga shi sama, har sai da mutane suka ga hasken hamatarsu (Manzon Allah da Ali), (kamar dai yaddda yan siyasa ke daga hannu) sannan yace: Yaku mutane, Allah shine Majibincin Al-Amarina, Niku nine majibincin Al-Amarinku, wanda na kasance a gareshi Majibinci to Aliyu majibijincinsa ne, Ya Ubangiji, ka jibinci wanda ya Jibince shi, kayi Adawa da wanda yayi Adawa dashi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, ka wulakanta wanda ya wulakanta shi, ka So wanda ya soshi, Ka Qi Wanda Ya Qishi, Sannan Ya ce: Ya Ubangiji ka Shaida, sannan basu rabe ba - Manzon Allah da Aliyu - Har sai da Wannan ayar ta sauka: "Yau ne na cika maku addininku, sannan na cika akan ku ni'imata, sannan na yardar akanku Addinin Muslunci (Ya zama addini a gareku)" Duba: Ma'ida (3).
.
- Sai Manzon Allah SAW yace: Allah mai girma Ne!, Akan kammala addini, da cikar ni'ima, da yardar Allah Ga Isar manzanci (na) da wulayar Aliyu.
.
- Wannan hadisin wanda ya faru a Ghadir, nassine bayyananne akan imamancin Ali, da fadin manzon Allah "Wanda na kasance a gare shi WALIYYI, to Aliyu ma WALIYYINSA ne" Ma'ana: wanda na kasance a wurinshi Shugaba to Aliyu Shigabansa Ne, AL-WALII Shine IMAMA.
.
- Wannan nassi ne akan WULAYAR Ali a cikin wannan Abun da ya faru a Ghadir yayin da Annabi ya tsayu kuma ya tara jama'a, wanda yawansu yakai dubu dari ko sama da haka, kuma yayin da (Annabi ya) nassanta imamancin Ali bayanshi sai addini ya cika da saukar Ayar nan ta cikin suratul Ma'ida (3) "Ta bagata ba sai na maimaita ta ba".
.
* Sunnah — "Zan Cigaba Insha Allah".
.
In Shaa Allah a darasi na gaba zamiji yadda Malamin Sunnah yayi bayani daki-daki, da yadda zai warware wannan hadin gero da masarar!
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
18/12/1438H