Meya Faru A Ghadeer //3
.
"A baya Mun Tsaya Inda Malam yake bayani dangane da karyar Shi'a akan saukar wasu ayoyi dake suratul ma'ida: aya ta 67, data 3, Yanzu zamu cigaba"
.
* Cigaba —"Malam yace Na Biyu: Amma dangane da abunda aka samu dangane da dalilin saukar fadin Allah: "Yaune na Kammala maku addininku, kuma na cika ni'imata akanku,.." Ma'ida (3), Lallai wannan aya an saukar da ita a ranar Arfa, Hajjul Akbar, kuma wannan rana ta kasance ranar Juma'a ne, ba wani abu bane boyayye, hakika hadisai ingantattu sun gangaro wanda bukhari da Muslum suka ruwaito da wasun su, ta hanyar Ibn Shihab: "Wani bayahude yace da Umar: lallai ku kuna karanta wata aya wacce da mu aka saukarma ita da mun riki (ranar da aka saukar da ita) Idi, sai Umar Yace: Ni nasan lokacin da aka saukar da ita, kuma nasan inda manzon Allah yake lokacin da aka saukar da ita, (itace) ranar Arfa ne, Wallah Ranar arface" sufyan yace: Na manta Ranar Juma'ace ko A'a: "sai ya kawo ayar: Ma'ida (3)".
.
- Wannan Ruwayar tana nuni akan lallai wannan ayar ta sauka ne akan manzon Allah Alhali yana Arfa, kuma dukkanin mu mun san cewa ranar arfa ta auke ne kafin ranar Ghadeer da wasu kwanaki, Tayayama zamu ce wannan ayar an saukar da ita a Ghadeer Khum ne? Bayan kuma Hakika ruwayoyi Mutawatirai daga Malaman Muslunci sun nuna cewa ta sauka ne kafin (Gadir) da wasu yan kwanaki?!
.
Amma abun mamaki, yadda abokin tattaunawa ya lanqwasa wannan Nassin ya nuna wannan ayar ta sauka ne akan Annabi, bayan Annabi ya nassanta Imamanci Ali, Bayan kuma na Rantse da Allah! (Bata sauka ba) don an nassanta Imamancin Ali ba, kuma ba'a Ghadir Kum ta sauka ba."
____________
Domin Karin bayani akan nassin da malam ya kawo dama wasu nassoshin da bai kawo ba sai a Duba:
- Bukhari: (45)﹑(4696)
- Muslum (3017)
- Turmizi (3044) Takhrijin Al-Bani
- Ibn Jareer (6/53)
- Asbabun Nuzul Qur'aniy (184)
____________
Malam Ya cigaba da cewa: "Abu na Ukku: Amma abunda aka samu dangane da abunda ya faru a ghadir (na labarin gaskia) shine: Lallai Annabi Mai tsira da Amincin Allah (Bayan ya gama aikin hajjinsa) ya kama hanyar madina shida yan madina (don komawa gida), sai ya gitta ta wata korama ta ruwa ana kiranta khumma - Wuri ne dake kan hanya tsakanin makka da madina - sai ya yada zango anan bisa al_adarsa ta tafiya yakan tsaya idan yana tafia don ya huta. Sai ya tsaya nan domin wanda ya baro baya su riske shi, sannan kuma ya samu hutu daga gajiyar tafia. (Anan ne) Mutane (wanda suka tafi tare da Sayyidina Ali yamen) suka koka akan Aliyu, akan tsananta musu dayayi, tare da cewa tsananta musu da yayi shine daidai.
.
Kissar da ta faru kuwa ta gabata (tun kafin fitan Annabi hajji) ita ce Lallai Annabi Mai tsira da Aminci Allah kafin ya tafi Hajjin bankwana, ya aika Aliyu Yamen domin ya tattaro zakka, sai Aliyu ya tarro zakkar, ya taho da ita zuwaga Annabi Makka, domin yayi hajji tare dashi, akan hanya Mutanen (da yake tare dasu daga sahabbai) sai suka buQaci suyi amfani da wannan abu daga zakkar (Sobada Suna gani ya halatta su taba wani abu daga gareta saboda daga cikin wadanda Allah yace aba zakka akwai masu yimata hidima) - Amma Sayyidina Aliyu Saboda Tsananin Takatsantsan dinsa - Ya Hanasu yin amfani da wani abu daga gareta, saboda bata kasance mallakinsu ba, ta kasance Hakkine na baitil mali, sai hakan ya tsananta a garesu, yayin da suka isa sai suka kokama manzon Allah.
.
- Manzon Allah kuma dayaga Aliyu shine akan gaskia, sai ya tsayu gaban mutane domin yayi musu bayani gaba dayansu, sai ya miqe a Ghadeer khum, ya tunatar da mutane Allah, Sannan ya Umurce su da Riko da Littafin Allah, sannan yayi musu wasici da Ahlul baiti, kuma Aliyu yana cikinsu.
.
Sannan Ya bayyana gaban mutane wadanda suka kawo karar (Ali) wurin Shi, sai Yace: "Wanda na kasance MajibincinSa to Aliyu ma majibincinsa ne" domin Qara karfafa yabonsa ga Imam Aliyu sai Yace: "Allah ka jibinci wanda ya jibince shi, Kayi kiyayya da wanda ya kishi"
__________
- Duba Silsila Na Albani (1750)
__________
Wannan Shine abunda ya faru a Gadir, kuma wannan (Koken na Sahabban da sukaje yamen da ali) shine yasa Manzon Allah yace: "Wanda na kasance majibincinsa to Aliyu Majibincinsa ne" (Ba karyar Shi_a ba nacewa Allah ne ya saukar da aya a nada Sayyidina Ali ba).
.
- Amma karin da (Masu kari ke karawa) da kara kuzu-zuta Lamarin wanda wasu ke sakawa a cikin hadisin Annabi, na fadinsu cewa: "Ya Allah ka taimaki wanda ya taimake shi, ka Wulakanta wanda ya wulakanta shi" wannan karine da bai inganta ba kuma bazai samu shigaba a wurin ma'abota Ilimi".
.
(Zan Cigaba)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
21/12/1438H