Subscribe Our Channel

Meya faru a Ghadeer //2
.
"A Jiya Mun Kawo Maganar Malamin Shi'a ga wanda ya bibiyi rubutun mu, yaji yadda, hujjar shi'a ta kaya, to yau Insha Allah zamu cigaba"
.
* Sunnah — "Abokin tattaunawata, Wannan ai hade-Hade ne na mabanbanta ruwayoyin kuma daban-daban, da Kuma wannan tadlisin (kokarin bayyanar da abunda bashi bane), (Wannan sai yasa), mai sauraro yayi zaton Abu daya ne, Yayi tunanin ba ruwayoyi bane mabanbanta, Al-Hali kowacce ta saukane saboda wani sababi (daya kebance ta), kuma a mabanbanta wurare.
.
Kuma hakika Abokin tattaunawa ta yayin wannan tadlisi, da hade-haden, da kokarin bankara ruwayoyi mabanbanta wadanda suka faru a mabambatan lokuta, kai kace Abu daya ne ruwaya daya ce, (acikin wannan bayanin nasa) yayi kokarin nuna cewa Allah ya umurci manzon sa da ya isar da (Sakon) Imamancin Ali ga mutane, Sannan yayi mashi wasici da Khalifanci ga Musulmai bayan shi (Annabi), da fadin Allah: "Ya kai Manzon Ka Isar da Abunda aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka.." Ma'ida: (67), sai manzon Allah ya tara mutane a ghadeer khum (Inji shi: Dan Shi'an), kuma ya isar masu da wannan sakon, bayan haka sai Allah ya saukar da fadinsa: "Ayau ne na kammala maku addininku..." Ma'ida: (3) (Duk wannan wai inji shi, shi dan shi'ar).
.
Malam ya cigaba da cewa: "Sai dai wannan hade-haden Ya sabama abunda yake shine gaskia gaba da baya, ba komai bane face Hade-haden mayaudara, don su yardar da (Mutane) son ciyarsu
.
Amma mu zamu wargaza wannan riyace-riyacen (na karya), muyi bayanin wannan hahe-haden da fadin (Dalilanmu Kamar haka):
.
- Farko: Abunda aka samu na dalilin saukar fadin Allah ta'ala: "Yakai Manzo ka Iyar da Abunda aka saukar zuwa gareka daga Ubangijinka...." Ma'ida: (67), Lallai Manzon Allah SAW ya kasance idan zai fita wani yaki daga cikin yakoka, yakan tsaida wani sahabi daga cikin sahabbansa domin yayi gadinsa daga makiya (Domin ya samu ya dan runtsa), har ya kasance wani dare, Allah ya saukar a gareshi wannan ayar: Ma'ida (67), Sai ya leko ta yar kofar hemarsa, sannan yace "Yaku mutane, Ku tartafi, Hakika Allah ya Tsare ni), Tun da aka saukar da wannan ayar Annabi bai kara rikar mai gadi ba, yana mai dogaro da kariyar Allah a gare shi.
.
- Har wata rana wani mutum yazo yace da Annabi bani takobinka na dan sunsuna, sai (Manzon Allah) ya bashi, Al-hali (Acikin ran wannan mutumin) nufinsa shine ya kashe annabi, sai Hannusa ya kama rawa (Kyarma), Allah Ya shiga tsakaninsa da abinda ke ran (Wannan) mutumin da Annabi (Ma'ana ya kare Shi) daga nufinsa, domin kariya ga Annabi Mai tsira da Amincin Allah.
.
- Wannan Ruwayoyi da suka gabata suna nuna cewa Lallai wannan aya ta sauka da dare ne, kuma ta sauka akan Annabi ne, Al-Hali shi yana acikin Hemarsa, kuma akan Makwancisa (Shimfida), wannan dalilin ne yasa Imamus Suwiydi yake cewa: "Wannan Ayar (ta sauka) da dare kuma akan shinfidar (Annabi)", ai ta sauka da dare akan Annabi, ta sauka kuma Annabi yana a halin kwance bisa shimfidarsa.
.
- Malam ya cigaba da cewa: "Ku duba fa kuga yadda Malamai ke dagewa wurin tantancewa da tahdidin lokacinda Ayoyi ke sauka, ta yaya zamu gafala mu jingina wannan dalilin da abunda ya faru a ghadeer, tare da jingina wani Al-Amarin kuma daban kamar yadda abokin tattaunawa ta yake riyawa.
.
______________
Ni Abu-Ammar nake cewa: "Malam yayi bayani a dunkule kuma gamsash-she ga Ma'abota Ilimi da Hankaltar shi, Wanda yake nuni akan karyar shi'a da suke cewa wannan ayar an saukar da itane don Imamancin Ali a ghadeer, bayan kuma hakan karya ne. don Haka domin karin bayani kan wadannan ruwayoyi Da Malam ya kawo sai a Duba:
- As-babun Nuzulul Qur'aniy: (192, 193) Na AbiSh Shaikh, da Ibn Hibban.
- Ibn Jarir: Ruwayar Ikrima, da Ibn Abbas (6/189)
- Ibn Kathir: (2/87 - 91)
- Ibn Hibban: (230)
- Mustadrak: (2/313), Turmizi (3046), As-Babun Nuzul Kur'aniy: (193).
__________
.
— Ayi Mun afuwa nan zan tsaya sai a darasi na gaba: "Ina bukatar Addu'ar ku Ina fatama da Mura mai tsanani, Allah Yaba duk mara lafia lafia mai Amfani Ameen".
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
19/12/1438H.
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter