Ko Kasan? /2
Addinin Muslunci addinine Mai kira da hadin kai da kaunar Juna, da girmama Juna. Shiyasa Ahlus-Sunnah Suka kasance Mafiya Rinjaye wurin hadin kai, domin wannan shine akidarmu Yayin da muka maida manhaji daya abun riko kuma abun bi ba tare da rarrabuwa da ku sabawa, Imamud dahawiy yana cewa:
"Kuma Muna bin Sunnah (Annabi SAW), da Jama'a (Tawagar Annabi: Sahabbai da tabi'ai da tabi'ut tabi'ina), Muna nisantar shuzuzi (kadaituwa da kebantuwa da wani ra'ayi ko akida), da Sabani (Na Bata), da Rarrabuwa (Kungiyoyin bata)" Duba: (Sharhul Akidatud Dahawi: 325/ Maktabatu Al-Hadyul Muhammadiy)
.
Amma Su Shi'a Sun farrake farrakewa tare da Sukan Junansu, Farko Lamari dai Shi'a Itace Kamar Yadda Ibn Taimiyya yake Fada Minjahus Sunnah (1/7,8): "Lallai Shi'a farko sun kasance ne a zamanin Aliyu, Sun kasance Suna girmama abubakar da Umar, Yayin da mai tambaya ya tambayi Shirik bn Abdullah Qadil Kufa, Yace dashi: Wanene Yafi Falala, Abubakar ko Aliyu? Sai yace: Abubakar, Sai Mai Tambaya yace dashi: Zaka fadi hakane Bayan Kuma Kai dan Shi'ane? Sai Sharik yace: Eh! Kuma duk wanda baice haka ba (daga cikin masu da'awar Shi'anci) to wannan ba dan Shi'a bane, Yace: Wallahi (Naga) Aliyu Ya hauwa wannan Minbarin (Na wani Icce ne) yana cewa: Ku Saurara Lallai mafi Al-khairin Wannan Al-Ummar bayan annabinta Shine Abubakar sannan Umar. Tayaya zan watsar da maganarsa (Inji Sharik)?, kuma tayaya zan karyata shi?, Wallahi Shi ba Makaryaci bane (Kenan Yan Shi'ar baya-Baya Suna karyata Aliyu, kuma basa daukar maganarsa!).
______________
Kenan Farko Yan Shi_a na gaskia Sune masu Akidar Abubakar da Umar Sunfi Aliyu, A'a su suna gabatar da Aliyu ne kawai akan Usman har ana kiran Firak din guda biyu da: (As-Shi'iyyu da Uthmaniyyu), Shi'iyy: Wanda ya gabatar da Aliyu akan Usman, Uthmaniyy: Wanda ya gabatar da Usman Akan Aliyu. Duba: HamiSh Maqalatil Islamiyyah, Na Ash-Ariyy: (1/65).
.
Daga Nan Shi'a Sukaita Farraka kungiyoyin bata na Shi'a Sukaita fitowa, masu zagin Abubakar da Umar da Usman, Masu Allantar da Aliyu, dama masu zagin Aliyun da Iyalan gidan Annabi, da kafurce kafurce Iri iri.
.
Kamar Yadda Mai Al-Farku Bainal Firaq (21) Ya ke cewa: "Sannan Rafida Suka rarrafa bayan zamanin Aliyu ya wuce, Manyan daga cikinsu: Zaidiyya, Imamiyya, kaisaniyya, Gulat..... Kowacce firka kana kafurta yar uwarta..."
.
Bagdadi Yana cewa: Sun kasu Firka Sha biyar, Sai ya Lisafosu, sannan yace kowacce firka tana sabawa yar uwarta Duba: Al-Farku Bainal Firaq: (53).
- Zamu fahimce Cewa dai babu hadinka, Asalima, zagin junansu suke, kamar Yadda Rafida Suka watsar da Zaidu Dan Aliyu zainul Abidina, don yace dasu yayin da suka tambaye shi game da Abubakar da Umar: "Ya nuna cewa sune mafiya girma bayan Annabi, kuma abokan kakansa"
____________________
Muyi duba cikin Imaman Shi'a
- Muhd Bn Abdullahi (SAW)
- Aliyu bn Abi Dalib Al Murtada
- Hasan Azzaki
- Husaini Ash-Shahid
- Muh'd hanafiyya (Dan Syyd Aliy)
- Aliyu bn Husain Zainul Abidina
- Muh'd Bn Aliyu Al-Bakir
- Ja'afarus Sadiq
- Musa bn Ja'afar Al-Kazim
- Isma'il Bn Ja'afar
- Muh'd Bn Isma'il (Kalifan Isma'il)
- Aliyu Bn Musa Arridah
- Muhd Bn Aliyu Al-Jawad
- Aliyunil Hadi
- hasan bn Aliyul Askari
- Muh'd Bn Hasan Al-Muntazar (Ma a haifeshi ba karya suke)
- Fatima Bn Muhammad Azzahara.
(Dukkaninsu bayin Allah ne na kwarai Amincin Allah ya kara tabbata a gare su baki daya da wadanda suka biyosu da kwatatawa, bada zagonkasa da Munafurci ba, Banda Al-Muntazar domin shi babau shi hasan bai haifi da waishi muhd ba, nan gaba mun dan kawo tatsuniyar a takaice)
____________
* Acikin Wannan Jerin Zamuga cewa Sun Wuce 12, kamar Yadda yan Sha Shiyu ke da'awa, to na kawo sune gwargawan wadanda na sani, Sannan Sun wuce Shabiyu ne gwargwadon Sabanin da Shi'awa Sukayi, domin akwa masu da'awar Imami 1, 4, 7, 12 da Sauransu!.
.
Allah yasa mu dace ya karemu daga Sharrin Shi'a da duk kungiyoyin bata Ameen (Zan cigaba)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
13/12/1438H.
Ko Kasan? /2
Subscribe Our Channel