Subscribe Our Channel

Hausa: "Idan ana sara a rika duba bakin gatari".
.
— Gaskia yana da kyau Iyaye, yayu, da malamai musamman malaman islamiyya suna bibiyar diyansu ko dalibansu suna lura da abunda suke ta'ammuli dashi musamman na littattafai musamman littattafan hausa na muslumci, domin dayawa kana koyar da yaro tarbiyya da ilimi amma kuma shi yana cen yana koyan wasu gurbatattun akidoji da kuma wasu bid'o'i, da dabi'o'i na daban.
.
— Misali: Yau na karbi wani littafi a hannun wata yarinya da bata wuce shekara 8 ba, amma ta iya karatun hausa sunan littafin (SANIN ADDINI A SAUKAKE) wanda ya rubuta bai sa suna ba, sunan mai yadawa Abdulhadi Dayyabu Na Alh. Nura (Kasuwar kurmi kano.) littafin cike yake da bid'oi da karairayi, bal ma littafin da bid'a ya fara, ba yabo ba godiya ga Allah da salati ga manzon Allah SAW. Sai yace.
.
(BAYANI A KAN TSARKIN FITSARI
shi ne mutum ya sanya zakarinsa a tsakanin yatsunsa sabbaba da ibhama (Wato wanda yake nuni da shi da babban dan yatsa) sai ya shudar dasu daga farkon zakarinsa har zuwa karshensa yana mai karkadawa zai aikata wannan sau ukku da sauki wajen tatsar da karkadewa sannan ya sa ruwa ya wanke).
.
— Kunga fa da abunda ya bude littafinsa dashi bayan basmala, wanda hakan kuma bid'a ne, Magabata Sun kasance suna kin hakan, Kamar yadda Ibn Abi Shaibah (1/178) ya ruwaito daga Ibrahimun Nakha'ii yana nuna karhancin hakan,
- Haka ibn Tambiyya a cikin Maj'mu'ul fatawa (21/107) yake cewa Yin hakan bid'a ne, harma yake nuna cewa fitsari kamar hantsar dabbace idan zakaita tatsa shi kuwa zaita fitowa.
- Shi kuwa Ibn Qayyim cewa Manzon Allah bai kasance yanayin irin wannan ba, har yake cewa bai kasance yana aikata irin wannan bid'o'i na Ma'abota waswasin(Shaidan) ba". Duba: Zadul Ma'ad (1/173).
.
— Kuma wani abun ban haushi idan kuka duba bayanin kwata-kwata ya kore shiriyar annabi SAW yayin yin tsarki a cikin bayaninsa, domin yace ayi wancen bid'ar sau ukku sai a wanke, bayan kuma wankewar itace ukku, kamar yadda Muslum (262), da Turmizi (16), da Abu-Dawood (40), da Nasa'i (1/18) da wasunsun suka ruwaito. Dama ita dama bid'a haka take.
.
— haka ya cika littafin da bid'a da wasu addu'oi marasa kan gado, hada wata addu'a ta kudubar daurin aure, data rada suna, kai saidai wanda ya karanta.
.
— Wasu na ganin wannan mas'alar mai saukice amma ni ina ganinta da girma sosai, domin har littafin shi'a na hausa na karba a wurin wata, a wannan ramada din har wani littafi na karba mai suna "Nafilolin dararen watan ramalan", Kasha haushi da dariya, ko wace raka'a da yadda akeyin da da suanan Allah da zaikai amfani dashi da kuma abunda zaka roQa.
.
— Gaskia yana da kyau a kula domin ni ina ganin mafi girman hanyar da yara tarbiyyarsu ke lalacewa a yanzu bai wuce abu ukku.
1- Littattafan banza
2- Fina-Finai
3- Social Media.
— Ya Allah ka karemu daga dukkanin sharrin duk wani abu mai sharri, mutumne ko ba mutum ba, ka karemu daga sharrin Makiyanmu Ameen.
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
08/10/1438H - 02/07/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter