Subscribe Our Channel

*DAGA BAKIN SHEIKH JA'AFAR*
.
"Dangin Abunda ke fitowa daga kasa shine Arziki ba man fetur ba, Idan kaga kasa(country) tana auna fetur a matsayin arziki watou jahilai sunyi yawa a kasar kenan, bayan ga kasar noma?

.

Shiyasa lokacin sarki faisal da amerikawa suka yi masa shakiyyanci, sai ya gayyaci shugaban amerika na waccen lokacin, ya shirya masa wani gari, a bayan garin riyad, gari ne kawai akayi.. Da bukkoki irin wanda larabawa keyi lokacin jahiliyyarsu, duk abunda ke a cikin garin wanda yake ala dabi'atihi ne ba tare da sa hannun wani bature ba, ba wutar lantarci, sai fitilar kwai sai aci bal-bal, babu komai sai dabino, sai shayi, sai naman rakumi, sai kaza, kayan fada yasa sojoji sukayi irin faretin nan da kayan fada na gargajiya da masu da takubba, da bindiga irin ta gargajiya dinnan ta toka.

.

Yace da amerikawa Wallahi idan kukace sai kun tursasa ni, naji manufofinku akan gabas ta tsakiya, a shirye nake rijiyoyin man fetur dina mu kone su mu koma irin wannan rayuwar da mukai kwana ukku dakai anan.

.

Yace: don nazone don inyi addini banzo ba don arziki, ko ba haka ba? Kuma da wanda ya rayu anan kwana ukku, tunda har na rayu anan kwana ukku ina shugaban kasa, kaima daag amerika kazo ka rayu anan kwana ukku, ma'ana: zamu.. Kowama zai iya rayuwa a wannan tsarin ko ba lantarki. Ina fatan kun fahimta?

.

Yana da kyau mu rinka fahimtar menene arziki da nassin Al-kur'ani da nassin hadisin Annabi SAW, yanzu gwabnatocinmu suna kula da noma ne? Suna kula da kiwo ne? Bama kirga noma ma cikin arzikin mu, amma idan ba haka ba jahar barno, jahar yobe, jahar, jigawa, jahar zamfara, jahar kano, jahar wanene kadai basun iya su ciyar da najeriya ba gaba dayanta, jahohi ukku kawai na arewa masu rinjayen musulmi in zasuyi noma da kiwo da gaske abunda abunda suke samu daga gwabnatin tarayya ya kasance sun sarrafa shi ga noma da kiwo kadai, da an daina yi mana dariya, ana cewa wai mu cima zaune ne, sai dai a hako man fetur mu kuma mu cinye komu sace, komuyi menene menene.

.

bayan mu mukeda arziki na gaske, mu muke da kasar noma! Sucen suna da kasar noma ne? In kaga an noma wani abu kwakwace, hm yo a cikin ku akwai wanda yake fatan yaci kwakwa? Wallahi nidai bana fatan inci kwakwa, bahaushe yace zakaci kwakwa ai ka gama yawo."

.

"Noma da kiyo shine farilla, wanda ba suba mustahabbi ne"
— Mal. Ja'afar Tafsirin suratul Bakara aya ta 21, Kasat na 3, shekara ta 2002, saukar Mai-duguri.
.
Allah ya jika malam da rahma, yasa muyi amfani da abunda suka bar mana gado na Ilimi, mu talakawa da shuwagabanninmu da masu kudinmu Ameen.
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
22/10/1438H, 16/07/2017M.
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter