Subscribe Our Channel

Daga Ayyukan Al-Kharin (Zul-Haj)
.
Hakika Hadisi Ya Gangaro daga Manzon Allah SAW, Kamar Yadda Ibn Majah Ya Fitar Hadisi Mai Lamba (277), da Waninsa, Da Sanadi Ingatacce, Kamar Yadda Yazo Littafin: "Ta'aZiimu Kadris Salah: 170" Tahkikin Babban Malami: "Abu-Malik Kamal Bn Sayyidis Salim", Manzon Allah Mai Tsira da Amincin Allah Yana Cewa: "Ku Tsayu (Akan Abunda na bar Muku: (Al-Kur'ani da Sunnah Ta), kada ku karkace (Daga Gare Su), Kuma ku sani Lallai Mafi Al-Khairin Ayyukanku (Itace) Sallah, Babu Mai Kiyayewa Akan Al-Wala Sai Mumini" Hadisin Thauban Ne Allah ya kara yarda dashi.
.
Imamu Muslum (379), da Imamun Nasa'i (2/227) da Abu-Dawood (1320), da Ahmad (3/59), Sun Fitar da hadisin Thauban Allah Ya kara yadda dashi, (akaro na biyu) Ya tambayi Manzon Allah Akan Aikin da zai shigar dashi AlJanna Sai Manzon Allah Yace dashi "Ina horonka da Yawaita Sujjada, Domin Lallai kai bazakayi Sujuda Ga Allah Ba, face Allah Ya Daga Darajarka, Ya kankare Maka Zunubanka da Ita..." [Wannan Hadisi Yana Nuni akan Falala da Girman Yawaita Sallar Nafila, Musamman A Lokuta Masu Girma, kamar Wannan Lokacin Na 10 Farkon Zul-Hajji]
.
Imamut Turmiz A cikin Sunan Nasa Ya fitar da hadisi (337), Da Mai Littafin Ta'aziimu Kadris Salah 156 Tahkikin Sayyidis Saalim, Daga Sahabi Abu-Huraira Allah ya kara yarda dashi, Yace Yaji Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah Yace: "Lallai farkon Abunda za'a fara yiwa bawa hisabi dashi Ranar Al-Qiyama, Itace Sallah, Idan Tayi kyau, To Hakika Ya Rabauta Kuma Ya Kubuta, Idan Ta baci, to hakika Ya Tabe Kuma Yayi Asara, Idan Sallar Farillarsa ta samu Nakasu, Allah Mai Girma da Daukaka Zaice: ku duba, Shin ko Bawana Yana da Nafila Domin a cikashe mashi Abunda ya rasa na Farillarsa? Sannan Sauran Ayyukanma Akan Haka" [Sannan Hadisi Yana Nusar Damu Falala Da Girma, tare da Fa'idar Sallar Nafila].
.
- Al-Imamul Maziriyyu Yace: Dabarani Ya Ruwaito Acikin Awsad' da Sanadi Hasan, Duba Attargiib: (572), Hadisin Abu-Huraira Yace Lallai Manzon Allah SAW Ya Gitta ta wani Kabari, Sai Yace: "Wanene Ma'abocin Wannan Kabarin?" sai Sukace: Wane Ne, Sai Yace: "Raka'a Biyu (Rak), Sunfi Soyuwa Ga Wannan (Ma'abocin Kabarin), Sama da Sauran Duniyarku (Duniya da Abunda ke Cikinta).
.
"Yan Uwa Wannan Lokaci Mai Tsada Yana da Kyau Mu Yawaita Ayyukan Al-Khairi domin Su zame mana Haske A Ranar Al-Qiyama, Su zame mana Sutra A ranar Nonan Asiri"
.
(Zan cigaba Insha Allah)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
04/12/1438H.
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter