Subscribe Our Channel

RIQO DA AL-KUR'ANI DA SUNNAH // 4
.
* Bayan ayoyi da hadisan manzon Allah SAW da muka kawo masu nuni akan bin Al-kur'ani da sunnar ma'aiki SAW, sannan kuma mun fara kawo maganganun magabata na kwarai kan wannan mas'ala, yau insha Allah zamu cigaba da kawo maganganun wasu daga cikin magabata na kwai, me sukace?
.
**IMAMU MALIKU BN ANAS R.T**
— Imam Malik asalin sunansa shi ne: Malik Bin Anas Bin Malik Bin Abi Amir, Abu Abdullah, Al-asbuhi, Al-madani, Imam Darul hijra, Hujjatul Islam, an haifi Imam Malik a shekara ta (93A.H) a Madina.
.
— Hakika an samu maganganun da dama daga bakin Abu-Abdullah Maliku Bn Anas akan wannan mas'alar wadanda ke nuni kai tsaye akan a aje duk wani ra'ayi koma bayan Maganar Allah data manzonSa SAW ga kadan daga ciki.
.
1 — Yake cewa "Kuma Lallai ni Mutum ne(Kamar kowa) Inayin kuskure kuma ina yin daidai, don haka kuyi duba cikin ra'ayina, duk kanin ra'ayin da yayi daidai da Al-Qur'ani da sunnah to ku rike shi, kuma duk ra'ayin da baiyi daidai da Al-kur'ani da sunnah ba to ku watsar dashi" Duba: Littafin Ibn Abdulbarri [Al-Jaami' : 2/32], da Littafin Ibn Hazmin [Usulul Ahkam : 6/149].
.
* Anan zamu kara fahimtar shifa maliku ba ma'asumi bane, zai iya bada fatawa amma kuma kuskure ne, domin shi ba wahayi ake masa ba, haka kuma zai iya yin daidai, wannan muka shine cikar mutuntaka ga duk wanda ba annabi bane ko manzon, domin sune ma'asumai kuma ana yi musu wahayi, wannan maganar tasa zata kara bayyana mana abunda maliku ke nufi itace:
.
2 — Yake cewa "Babu wani daya bayan manzon Allah face ana daukar maganarsa (ayi aiki da ita), kuma ana watsar da maganarsa (aki aiki da ita), sai manzon Allah SAW" Duba: Littafin Ibn AbdulBarri [Al-Jami' : 2/91], da na Ibn Hazmin [Usulul Ahkam : 6/148 da 179]
.
— Wadannan maganganu na maliku guda biyu suna nuna cewa za ai aiki da wasu daga cikin maganganunsa idan sun dace da shari'a haka kuma za'ayi watsi da wasu daga maganganunsa don sun sabawa shari'a, ba maliku ba hakan take akan kowa bayan Manzon Allah SAW, don haka aiki da Al-kur'ani da sunnah shine wajibi, amma ra'ayin wani idan ya saba musu to wajibine a watsar da ra'ayin. Allah yasa mu dace Ameen. (Akwai cigaba).
.
— Abu-Ammar
05/07/1438H - 02/04/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter