Subscribe Our Channel

RIQO DA AL-KUR'ANI DA SUNNAH // 3
.
* Bayan ayoyi da hadisan manzon Allah SAW da muka kawo masu nuni akan bin Al-kur'ani da sunnar ma'aiki SAW, yau insha Allah zamu kawo maganganun wasu daga cikin magabata na kwai, me sukace?
.
**IMAMU ABU HANIIFAH R.T**
— Imamu Abu-Haneefah Nu'umanu dan Thabit Allah yayi masa rahma, Hakika an samu daga dalibansa, da abokansa sun ruwaito maganganun wadanda dukkansu suke akan abu guda daya, shine Wajabchin Riko da sunnah da barin riko da maganganun wasu mutane koda ko sune, da kadan daga cikin maganganunsa:
.
1 — Yace: "Idan hadisi ya inganta to shine mazhabarmu" Duba littafin Ibn Abidina: [Al-hashiyyah : 1/63].
* Ma'ana: Idan hadisi ya inganta, ya sabawa mazhabarmu , to kuyi aiki da hadisi, ku watsar da maganganun mu, domin muma wancan hadisin shine mazhabin mu. Wannan hikayar, hakika imamu ibn abdulbarri ya naqalto ta daga Abu-Haneefah, da waninsa.
.
2 — Yace: "Baya halatta ga wani mutum, da yayi riko da wata maganarmu, matukar bai san inda muka cirato ta ba" Duba littafin Ibn Abdulbarri [Al-Intiqa'u Fi fada'ilil A'immatul Arba'a: 135], da Littafin Ibn Qayyim [I'ilamul Maukifiin : 2/309]
.
— A wata ruwayar cewa yayi: "Haramun ne yin fatawa ko aiki da maganarmu, akan duk wanda bai son dalilin mu na yin wata maganar mu ba.
— A wata ruwayar ya kara da cewa: "Ni mutum ne (kamar kowa). Zan iya fadin magana yau gode in dawo akanta(in warware ta)".
.
* Ma'ana Idan ya kasance baka san dalilinsu na yin wata magana/fatawa ba, to baya halatta a gare ka kayi aiki, ko fatawa da maganarsu, wannan wani ta kunkumi ne don gudun daukar maganarsu ka rattabata inda ka gadama, ba tare da sanin inama maganar ta dosa ba.
.
3 — Yace da Abu Yusuf "Kai conka ya kai ya'akub ! kada ka rubuta komai da kaji daga gare ni, Hakika ni zan iya daukar wani ra'ayi kuma gobe in chanza daga gareshi, ko kuma gobe in dauki wani ra'ayi jibi kuma in chanza daga gare shi" Duba Littafin Sha'arani [Al-mizan : 1/62].
.
4 — Yace : "Idan Nayi wata magana da ta sabawa littafin Allah (Al-kur'ani) da sunnar manzon Allah SAW, ku watsar da maganganu na(kuyi aiki da Al-kur'ani da sunnah)" Duba Littafin Fallaniy [Al-Iqaz : 50].
.
* Wannan yake nuna taka tsantsan wurin magabata dan gane da nisantar kaucewa Al-kur'ani da sunnah, shiyasa suke yawan maimaita ire-iren wadannan magan ganun lokaci zuwa lokaci.
.
— Domin neman karin bayani a dunkule duba Littafin Muhammadun Nasurud dinil Al-baniy: [Siffatus-Salatun Nibiyy : 41 - 43] ko kuma Littafin Abu-Malik kamal ibn Sayyid Salim [Sahihu fiqhus Sunnah : 33].
.
Allah ya bamu ikon riko da Al-kur'ani da sunnar Manzon Allah SAW a bisa fahimtar magabata na kwarai (Akwai cigaba).
.
— Abu-Ammar
26/06/1438H - 24/03/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter