RIQO DA AL-KUR'ANI DA SUNNAH // 1
.
Dukkan yabo da godia sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa, muna neman taimakonsa da agajinsa, wanda Allah ta'ala ya shiryar babu mai iya batar dashi, wanda Allah ta'ala ya batar babu mai iya shiryar dashi, Salati da aminchi da daukaka su kara tabbata ga fiyayyan halitta dan gatan Allah, wanda Allah ya bawa kwangilar bayanin Al-kur'ani, Annabinmu Muhammad SAW, da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar tonan asiri.
.
Bayan haka kasani yakai dan uwa lallai riko da dukkanin nassoshin al-kur'ani mai girma, da aiki dasu, da kuma sunnar Ma'aikin Allah Abu-Kasim SAW wajibi ne ga dukkanin wani mukallafi, kuma mai hankali.
.
* Allah ta'ala yana cewa: "Ku bi abinda aka saukar zuwa gareku daga ubangijinku, kuma kada kubi wasu majibinta baichin shi. Kadan ne suke ganewa" [A'araf: 3].
— Abu-Malik Sayyidus Salim: "Abunda Allah yake nufi da abunda aka saukar zuwa gareku shine Al-kur'ani, da kuma sunnar dake bayanin sa, ba tare da ra'ayin wani ba". [Sahihu Fiqhus sunnah 1/26].
.
* Kuma Allah ta'ala yana cewa: "Kuma idan akace dasu kuzo zuwa ga abunda Allah ya saukar, kuma zuwa ga manzo, zakaga munafukai suna kange mutane daga gareka, kangewa" [Nisa'i : 61].
— Wannan aya na nusar damu cewa, duk lokacin da aka kirayi mutane zuwaga Al-kur'ani da sunnar manzon Allah SAW, babu samu guje masu, da kauce masu, sai munafuki, hakama wanda ke umurni da guje musu.
.
* Kuma Allah ta'ala yana cewa: "...Idan kunyi jayayya cikin wani al-amari, to ku maidashi zuwa ga Allah da manzon Allah, in kun kasance kuna masu imani da Allah da ranar karshe." [Nisa'i : 59].
— Mai da al-Amari ga Allah shine komawa ga littafinsa Mai Tsarki, Maida Al-Amari zuwa ga manzon Allah kuwa, bayan mutuwarsa shine komawa zuwa ga sunnarsa, sai Allah ya ta'allaka hakan da imani dashi da ranar karshe, da hakan zamu fahimci cewa duk wanda bai maida lamarinsa zuwa garesu ba, to ba shakka wannan baizama daga masu imani ba.
.
* Sannan Allah ta'ala ya kuma cewa: "Kuma ku bi mafi kyaun abinda aka saukar zuwa gare ku daga ubangijinku, Tun kafin azaba ta riske ku, a afke, Kuma ku baku sani ba". [Zumar : 55].
— Babu kokwanta cewa Lallai mafi kyauwun zance shin Al-kur'ani mai girma wanda aka saukar daga wajan ubangijin mu, kamar yadda akan ya tabbata a cikin hadisin manzon Allah SAW, da kuma sunnar dake bayyanashi filla-filla, hakika duk wanda ya bishi zai shiryu, wanda kuma ya ki binsa zai bace, sannan kuma azaba zata riske shi, ba tare da yana sane ba.
.
* Kuma Allah ta'ala yana cewa: "Kuma abunda manzo yazo muku dashi to ku rike shi, wanda kuma ya haneku akansa to ku hanu, kuji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin ukuba ne" [Hashir : 7]
— Wannan ayar tana umurtar mu da bin Al-kur'ani da abunda yayi bayanisa watau sunnah manzon Allah, sannan tana tsoratar da duk wanda yaki yin aiki dasu, babu ma kamar wanda yake ganin ra'ayin wani mutum ya isar masa.
.
* Kuma Allah ta'ala yana cewa: "Hakika abun koyi mai kyau ya kasance a gareku acikin sha'anin manzon Allah, ga wanda yake kwadayin lada a wurin Allah ranar Karshe, kuma ya ambaci Allah da yawa" [Ahzab: 21].
— Da wannan yazame mana wajibi koyi da manzon Allah matukar musan dacewa da rahmar Allah a ranar Hisabi.
.
Kuma Allah ta'ala yana cewa: "To Aa'aha!!! Ina rantsuwa da ubangijinka, bazakuyi imani ba, har sai sun yarda da hukunchin ka na daga abunda suka samu sabani tsakanin su, sannan kuma bazasu ji wani kunchi a cikin zukatansu ba, daga abinda kayi musu hukunci, kuma su sallama, sallamawa". [Nisa'i : 65]
— Allah yayi rantsuwa a cikin wannan ayar domin ya nuna mana girman abunda zai biyo bayan rantsuwar na umurni ko hani. Allah yana fada mana cewa lallai bamuda imanai matukar bamu yarda da hukuncin manzon Allah ba, a takaice dai matukar bazamu sallama ba akan hukunce-hukunce shari'a ba.
.
(Akwai cigaba)
Abu-Ammar.
20/06/1438H. - 2017M.