Subscribe Our Channel

KA GODEWA ALLAH DAYA SHIRYAR DAKAI.
.
kwanakin baya Allah ya hadani da wani matashi, mai ragaggen tunani da shirya, jahilci kuma yabi ya mamaye kaso mafi girma da tsoka na zuciyarsa. Na yi mamaki matuka har naji kamar nayi kuka, amma da na fahimci lallai bashida karatu kona sisi saina tausaya masa, nakuma bashi shawarwar kamar yadda zan fada nan gaba, amma sai yaki karbar shawarata, da kuma fadin kalamai na jahilci, hakan yasa na kaurace masa saboda kada lafuzzansa sukai yayi furucin da yafi karfin imaninsa, nayi masa addu'a ta shiriya dashi da ire-irensa. Ga dai yadda abun ya kasance.
.
Ina cikin rubutu sai na budo wani rubutu wanda akayishi da haruffan larabci an sanya "Abakar" sai abokinsa ya karanta wannan rubutu cikin wasa sai yace kaidai nasan ba zaka iya karanba, yake cewa ya kamata ka koma islamiyya, sai yace shi Allah ya tuba, islamiyya ai ya wuceta. Sai nace kai yanzu kana nufin duk wani hukunce-hukunce ibada ka sansu, kuma wane guzuri kayiwa ranar lahira da kuma tambayoyin kabari.
.
Sai yace dani "Shi ai yasan yana da ruhun amsa tambayoyin kabari, domin yasan duk mai tsarkakakken ruhi to zai amsa tambayoyin kabari", tirkashi... Bugu da kari kuma dana kallesa sai nalura da cewa yana fadin maganar ne har a zuciyarsa.
.
Nayi timm nace dashi gaskia indai wannan ne tunaninsa, to gaskia yana cikin barazana, domin ya sanifa neman ilimi wajibi akan duk wanda ya aminta da muslumci a matsayin addininsa, ya murje ido akan shidai yana kan bakansa na baya. Abun ya daure mun kai sabida irin magan-ganun da yake, da yake lecture ne muke, sai lecturern yake mana nasiha akan yan sara suka, da daba...
.
Nan ma sai ya wata barin maganar yake cewa haka nan kawai ba gaira ba dalili a datse maka rayuwarka lokacinka baiyi ba, nace kamarya ai idan kaga ka mutu kota wane hanya ne lokacinka ne yayi, yace wallahi karya ne, lokacinka ne baiyi ba kawai yan bakin ciki zasu kasheka, da basu kasheka ba wayasan iya kwanan da zaka kara gaba.. Kuma ya cije akan ra'ayinsa.. Hakan yasa na kyaleshi. Sai nace amma wane gari kake?
.
Sai yace jibia nace amma hostel kake ko yace aa amma ya kama daki, nace to sai yaushe zaka tare sai yace jira yake sai sunyi fada da babansu, ya kwaso kayansa yace ga guntun kejinka nan... Sannan ya tare hostel,.. Nayi dariya nace karya kakeyi baban naku zakuyi fada dashi yace eh menene?
.
Nace aiko ka shirya cika akwatinka da C'0, budan bakinsa sai cewa yayi kawai don nayi fada da babanmu to miye, yana mai nuna kankantar abun, nanfa na nuna masa matsayin iyace a muslunci da irin yadda allah yake yawan gwama kadaitashi da kyatata masu, hakama a hadisan manzon Allah, abun yaci tura zuciyarsa ta bushe kamar kasarda tayi shekara 100 ba ruwa ba inuwa..
.
Karshe dai sai kaurace masa nayi na bar masa mazaunin, saboda kazaman kalamansa da bana iya maimaitasu.
.
Hakan yasa na dade zaune ina tunani da zullumi da mamaki, nayiwa Allah godia, akan halittani dayayi mutum musulmi kuma sunniy mai neman ilimin addini dana zamani, nace asheni ba jahili bane.
.
Hakan kuma ya karasa na hankaltu da wani abu dayawa adan zaman danayi dashi wanda bai wuce awa daya da rabi ba, na gane cewa dukiya ba ita bace baiwa ko daukaka, aa Allah ya yowa nagari mai kaunar iyayansa mai kuma daa da biyayya ga dukkanin iyakokin Allah, domin yaron a hannunsa wayar 37k wai secondhand cema, ga laptop.. Ga mashin. Amma duk gabanza.
.
Abun haushima baida wayewa a zamanance da zai iya sarrafa kayan kimiyya daya mallaka a zamanance... Ni inaga iyawa tafi samu domin in ka iya zaka samu.
.
Ya Allah ka kara mana hasken ilimi da biyayya ga dokokinka ka kara mana so da kyautatawa iyayen mu, ka kiyaye mana imanin mu Ameen.
.
Abu-Ammar
18/2/2017M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter