Subscribe Our Channel

WANENE SARKIN MUSULMAI MU'AWUYA DAN ABU SUFYAN (R:A) DA YAN SHI'A KE ZAGINSA – fitowa ta Biyar (5).
************
* © ZAUREN SUNNAH
**
cigaba na Biyar - 5
******
9). TARIHIN SARAUTA A RAYUWAR MU'AWUYA R.A?
* Game da sha'anin sarauta mu'awuya ya dade da tunaninta a ransa tun ranar da manzon Allah SAW yace masa; "yakai mu'awuya idan ka jibinci wani al'amari kaji tsoron Allah kuma kayi adalci". [Duba wannan bushara da Annabi SAW yayi masa a littafin mus'nad na imamu Ahmad hadisi na - 16872 da Siyar A'lam al nubala (3/131)].
*
°
* Wannan yana cikin karamomin Manzon Allah SAW. Domin kuwa mafi yawan rayuwar mu'awuya wacce takai tsawon shekaru 78 yayi ta ne yana jagorantar Al-umma tun baikai shekara Talatin ba ya fara jagorantar Kwamandan soja. A hankali haryakai matakin Gwabna wanda yayi shekara Ashirin 20, sannan ya zama sarkin musulmai na duniya baki daya na wasu shekarun ashirin din.
*
°
* Mutum na farko daya fara jibinta mu'awuya da sha'anin mulki shine Abubakar As-siddiq a lokacin da ya shugabantar dashi ga wata runduna da zata kai gudummawa ga dan uwansa yazid dan abu sufyan, daya daga cikin jagororin hudu da suke yaki a kasar sham.
*
°
* Mu'awuya ya cigaba da yaki a karkashin tunar dan uwansa inda bajintarsa tasa aka dunga shugabantar dashi ga kana nan rundunoni kuma Allah yana bashi nasara.
*
°
* Daga baya a zamanin sarkin Musulmi umar dan khaddab akai umurni ga yazid daya shugabantar da kanin nasa (mu'awuya dan Abu Sufyan) don cin garin Qaisariyyah. ya tafi kuma Allah ya bashi nasara Yacisu da yaki.
*
°
* A shekara ta goma sha takwas da bayan hijira sai akayi wata annoba akasar sham wacce ake kira da Amwas, wacce tayi sanadiyar mutuwar manyan kwamandojin yakin kasar. Umar dan khaddab R.A kuma ya dauki duk ayyukansu ya damkama mu'awuya. Saboda jarumtarsa da kokarinsa [Wannan Annoba tayi sanadiyar mutuwar sama da mutum dubu ashirin da biyar (25,000) a cikin dan kankanen lokaci Duba Almukhtasar fi Akhbaril Bashar na Abul-fida. Zaka sami littafin a duniyar yanar gizo a wannan maballin; www.alwarraq.com]
*
°
* A lokacin wani rangadi da khalifa Umar R.A yayi a kasar. Yayi mamakin ganin irin tsarin da mu'awuya ya shimfida na sarauta acikin kasaita a cikin wannan kasa. Mu'awuya kuma bisa hikimar da Allah ya bashi ya gamsar da khalifa umar akan dacewar hakan, bisa kasancewarsu kusa da kasar abokan gaba wadanda ake so su kasance musulmi nada wani khawarjini a idonsu.
*
°
* A anan zamu dakata, zuwa lokaci na gaba zamu dasa a kan wannan gaba sannan muyi bayani akan karya shi'awa akan fadinsu na cewa mu'awuya saunane, sannan babu wani abu da ya amfanar da muslumci da musulmai sai barna wanda karya aka masa kuma gashi karara muna gani a fili kuma a ilimince. Allah ya datar damu Ameen
*****
* A Nan zamu tsaya sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu dasa daga inda muka tsaya insha Allah.
**********
*
**********
Dan Uwanku; Engr. Ibrahim Yunusa Abu-Ammar.
*************************
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter