Subscribe Our Channel

WANENE SARKIN MUSULMAI MU'AWUYA DAN ABU SUFYAN (R:A) DA YAN SHI'A KE ZAGINSA – fitowa ta hudu (4).
************
* © ZAUREN SUNNAH
**
cigaba na hudu - 4
******
7). GUDUMMAWAR SA GA ADDINI A ZAMANIN ANNABI?
* Mu'awuya na daya daga cikin sakatarorin (Marubutan) Manzon Allah SAW ya kuma samu kyakykyawar addu'a a dalilin kokarinsa, inda manzon Rahama ya roka masa Allah ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, ya shiryar da mutane dashi. [Duba; Aljami'i na Turmizi da Al'shari'a na Al Ajurri (5/2437) kuma isnadin ya inganta].
*
* Mu'awuya yana daka cikin baraden yakin hunaini, Wanda Allah ya shede su da imani kuma ya bada sanarwar sakarda natsuwa akansu a cikin suratut tauba [Duba; Tauba:Ayata 26]. Yana kuma cikin mutanen da Allah yayiwa AlQawarin Al-husna wadda itace Aljanna, saboda sun ciyar da dukiyarsu saboda Allah bayan cin garin makkah. [Duba; Hadeed;ayata 10]
*
* Haka kuma ya halarci sauran yaqe-yaqen Manzon Allah SAW wanda ya gudana bayan anyi fatahu makkah, kamar yakin Da'ifah, Yakuma samu martabar kasancewarsa shugaba na farko daya Kaddamar jihadi a teku, kuma manzon Allah SAW ya yabama wadanda zasuyi yaki akan teku, yayi murna da Allah ya nuna masa su zazzaune kamar sarakuna akan gadaje. [Duba; Fathul bariy; (6:22)].
*
8). TARIHIN JARUMTAKAR SA?
* An haifi mu'awuya ne kafin shekaru biyar da fara wa'azin muslumci. Don haka bai shaida mafi yawancin rikicin da aka sha fama ba a farkon al-amari. Koda akazo yakin badar yana akan addinin iyayansa, kuma ya kai shekaru ashirin amma bai halacci yakin ba kannansa ne sukaje hanzalah da amru. Suna akan kafirci aka kashe na farko, aka kuma kama na karshe.
*
* Abinda tarihi ya bayyana shine halartar da yayi a yakin khandaq wanda mushrukai sukai hadin karfi don su karya muslumci, sai Allah ya tarwatsasu ya aiko musu da iska mai karfi ya hirgitasu, suka koma akan zabin kanasu. Kamar yadda suratul ahzab tayi sharhi.
*
* Bayan muslumtar Mahaifinsa Abu-Sufyan bayan da aka bude makka, Duk iyalan gidansu sunyi hijira zuwa madina wurin Manzon Allah SAW. Don Haka mu'awuya ya samu damar yin sauran yaqe-yaqe Manzon Allah bayan fatahu kamar yadda muka fada.
*
* Wannan ke nuna maka yan shi'a basu da wata masoka akan mu'awuya. Sannan madamar ka fahimci wanene mu'awuya. To hakika zakasan cewa yana daga manyan akidun yan shi'a kage da kazafi, matukar bakabi akidarsu ba.
*
* Ga misalinan ga baba PMB Buhari, suna ta jifarsa da karya da karairayi, da Qazafe-Qazafe, kwai don bai faranta musuba, baibi abinda su sukeso ba. Kuma wannan akidace ta yahuda wa kamar yadda Allah ya fada acikin suratul bakara "Kuma yahudawa da nasara bazasu taba yarda da kai ba, har sai kabi akidojinsu (idan kaga sun nuna maka yarda to hakika yaudarace da sannu zaka gane)....". Allah ya tsare mana imaninmu Ameeen.
*****
*****
* A Nan zamu tsaya sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu dasa daga inda muka tsaya insha Allah.
**********
*

**********
Dan Uwanku; Ibrahim Yunusa Abu-Ammar.
************************
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter