LALLAI LOKACI KAMAR TAKOBI NE HAKA KUMA ZARAR BUNU NE.
.
Dayawa daga cikin mutane "Musamman matasa" sukan samu lokaci mai cikakkiyar kuma nagartacciyar dama wacce ya kamata ace sunyi amfani da ita wurin ciyar da kansu gaba da kuma Al-Ummarsu.
.
Amma kash sukanyi watsi da wannan dama suki godewa Allah shikuma ubangiji sunnanrsa ce Idan ka gode masa zai kara maka. [Ibrahim: ayata 7].
.
Yayin da tunaninka ya dawo kan wannan dama sai tace inaaa ai bata san haka ba, domin ita ta gaji da jiranka har ta fece abunta.
.
To nan nakefa zai fara dama na sani nayi amfani da damata, gashi yanzu ta kubuce mini, ita kuma na dama ance keyya ce, shi kuwa lokaci tamkar maganace da idan ta fito daga baki bata komawa, sai fa idan har rakumi zai iya gittawa ta kofar al-lura.
.
Ni a nawa tunanin idan kana/kina matashi/matashiya babu wani babban abun girmamawa a wurin ka dayafi lokaci.
.
Da ace mun san muhimmanci lokaci da mun riki soyayyarsa kamar yadda muka rike son ruhin da dashine muke gudanar da rayuwarmu mai cike da nadama da asara.
.
Ka gina lokacinka bisa wani tsarin kanka, Allah shine mai tsara dukkan komai, sai dai mu sani cewa:
— Wurare da dama Allah ya nuna man idan muka mike sannan kuma kuma dogara gareshi zai taimaka mana.
— Ba laifi bane don kace kana son ka gudanar da rayuwar ka bisa tsari kaza-da-kaza matukar kace insha Allah, kamar yadda Allah ya umurci manzon Allah a cikin suratul kahfi.
— Manzon Allah SAW yana cewa: "Babu abunda ke tunkude kaddara sai addu'a, sannan babu abunda ke kara tsawan rayuwa sai da'a".
— ka sawa kanka aminci da dogaro da Allah kawai ka cigaba da tafiya, ina da yakinin Allah zai taimake ka, nidai fatana gareku matasa ku tsaya daidai Yadda Allah ya tsayar daku kada ku zurfafa.
.
Abu-Ammar
28/02/2017M.