[INUWAR SUNNAH (1)] HASKEN ILIMI A RAYUWA KASHI NA BIYU
******* *******
°°°°°HASKEN ILIMI A RAYUWA°°°°°
• Ka nemi Ilimi Kamar Yadda kake neman kudi ko acin abincinka/shanka, sannan ka sanar dashi kamar yadda kake biyawa kanka bukata yayin da ka nemeta.
• Shi neman Ilimi yana kasancewa ne a dukkanin gabobin rayuwar ka, haka shima ilimi ana yadashi a dukkanim gabobin rayuwa, damin raywa tana gudanuwa ne cikin neman ilimi da yada shi.
.
• Neman ilimi wajibi ga dukkan wani musulmi kamar yadda Abul-kasim SAW yake fada a cikin wani hadisinsa ingantacce Hadisin Anasu Dan Malik, wanda bukari da muslum suka fitar yake cewa "Neman Ilimi Farillane akan kowanne musulmi" a wata ruwayar "musulmi namiji da musulma nace".
.
• Wajabcin Neman Ilimi wajabci ne na kifaya watau wani zai iya daukema wani. Ma'anar hakan Shine;
- Idan Ya kasance A gari ko yanki (Al-Qarya) babu mai ilimi, ko kuma babu wani ilimin da mutane ke bukatuwa zuwa gare shi, misali babu malamai kwata-kwata, ko kuma akwai amma basada wani ilimin da yake wajibi ga Al-umma musulma kamar ilimin rabon gado, zakka, da sauransu, to adaidai wannan gabayazama wajibi ga kowanne musulmi dake wannan yankin (Al-Qaryar) babba ko karami, tsoho ko matashi, da yaje ya nemo wannan ilimin, ko kuma a wakilta wani yaje ya nemo.
.
• Shidai Ilimi kowanne Shine ginshikin rayuwa, matukar Al-umma ta wayi gari babu ilimi acikinta, ko shakka babu zakaga wannan al-ummar ta wayi gari cikin rashin natsuwa da tsarin rayuwa, idan kuwa akwai ilimin amma ba'a aikin dashi to hakika tsanani da mawuyacin hali.
.
• Misali idan muka dauki nan gida najeria yanki hausawa zamuga irin yadda muka dauki al-ada kan addinin mu da muhimmanci akan sha'anin aure. Ta yadda muka kakabawa kanmu wasu abubuwan da amatsayin mu ta musulmai bai kamacemu ba, sai muka wayi gari cikin tsananin nadama da wahalar da saidai Allah ya kiyaye.
.
• Don Haka mu sani cewa kamr yadda neman Ilimi yake wajibi to aiki dashima wajibi ne, Da fadin Annabinmu SAW "Kwarin Azaba ya tabbata ga wanda ya sani sannan ya take sani".
.
• Sannan Mu sani cewa neman ilimi wajibi ne, wannan kuma shi ilimi Haske ne, kuma shiriya ne kamar yadda jahilci duhu ne kuma batane, Shiyasa annabin rahama ya umurce mu da neman ilimi, a hadisin Anasun Bin Malik Manzon Allah SAW yake cewa; "Ku nemi Ilimi koda zuwa birnin Sin(China) ne".
.
Anan zamu dakata sai kuma wani darasin idan Allah ya kaimu zamu dasa akan wannan mas'ala ta ilimi insha Allahu ta'ala.
.
○
○
↓↓↓↓↓
Rubutawa;
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
***