Subscribe Our Channel

WANENE SARKIN MUSULMAI MU'AWUYA DAN ABU SUFYAN (R:A) DA YAN SHI'A KE ZAGINSA – fitowa ta biyu (2).
************
*
*
☼ Tambihi; A darasi na farko wanda ya gabata mun kawo wasu wadanda suke kamada manzon Allah SAW a siffata jiki, karin bayani; saboda kada wasu suyi tawili tahanyar juya wannan magana da wani wanda basu ba, don haka ga cikakken sunan su.
1* Hasan Dan Ali Dan Abu-Dalib Jikan Manzon Allah
2* Hussain Dan Ali Dan Abu-Dalib Jikan Manzon Allah
3* Shakru Dan Harbu Dan umayyah Mahaifin Mu'awuya
4* Sa'ibu Dan Ubaidu Kakan Imamush-shafi'i.
☼ Dukkansu sunada dan gantaka ta jini da manzon Allah SAW ta kusa-kusa.
************
Cigaba; - 2
************
6). IYALAN SA?
* Mu'awuya ya auri mata kamar haka;
1- Maisun Diyar Bahdal, Yar kabilar Kalbu, itace Uwar dansa Yazidu, kuma ta haifi wata yarinya data mutu qarama.
2- Kitwah diyar Qurazah taje yakin Qubrus Tare dashi kuma acan ta rasu, daga nan ne aka aurar masa da Qanwar ta.
3- Fakhitah Dayar Qurazah (kanwar wacce ta rasu a yakin Qubrus "kitwah") Ta haifa masa Abdurrahaman wanda ya mutu yana karami, da kuma Abdullahi, Shi kuma ya tashi da Wauta.
4- Na'ilah Diyar Umarah yar kabilar kilabu, yarabu da ita sai ta auri habibi dan maslamah al-fihri, daga baya kuma ta auri nu'umanu dan bashir.
5- Qaribatu Diyar Abu Ummayah yar uwar uwar Muminai Ummu Salamah, mijinta na farko shine sayyidina Umar ya aureta a jahiliyya sai ya rabuda ita sai ta auri mu'awuya shima daga baya ya rabu da ita sai ta auri Abdurrahaman dan Abubakar.
* Mu'awuya yaya hudu kawai ya haifa, yazidu da kanwarsa da ta rasu, sai Abdurrahman da Abdullahi, Abdullahi Ya tashi da wauta, Abdurrahman kuma ya mutu yana karami.
* Don haka bashi da wani da kamar Yazidu.
* Mu'awuya ya daina haihuwa tun lokacin da ya samu rauni sakamakon yunkurin kisan da khawarij sukayi masa. A lokacin ne wani likita ya bashi zabi tsakanin yimasa magani da wuta (lalas), da kuma bashi wani maganin da zai hanashi haihuwa, sai mu'awuya ya zabi na karshen.
7). MUSLUMTAR SA?
* Mu'awuya ya muslumta yana da shekara a shirin da biyar 25, A shekara ta bakwai bayan hijira, lokacin da manzon Allah SAW yazo Makka umrarsa ta hudaibiyyah. Da farko ya boye muslumcinsa don tsoron mahaifinsa. Amma daga baya Abu Sufyan ya gane, kuma ya ringa ce masa, dana Yadizu (yayan Mu'awuya) ya fika don yana kan addinina.
*
* YAN ADDININ SHI'A SUNA FADIN MUMMUNAR MAGANA AKAN MU'AWUYA A DAIDAI WANNAN GABA TA MUSLUMTARSA SUNA CEWA; shi munafuki ne domin ya boye muslumcinsa. Da ya muslumta da gaskia da ya bayyana imaninsa da Allah da manzonsa.
*
☼ FARKO DAI MUNSAN SUWAYE MUNAFUKAI A ZAMANIN MANZON ALLAH; Sune wadanda suke boye kafurcinsu a zukatansu su bayyana musluncinsu a baki, a karka shin daular muslumci, sannan sunyi hakane don tsoron kada, muslumci yayi karfi ya mamaye su, wasu kuma don su kawowa addini matsala, kenan sunayin munafuncinsu cikin al-umma musulma, wanda sunada halaye da ake ganesu masu yawa daga cikinsu akwai;
* karya; musamman lokacin fita yakunan muslumci, sukanzo suyiwa annabi dadin baki da karairayinsu suna fadin wasu uzrori na karya.
* rantsuwa akan karya kamar yadda, yazo a hadisin ibn abbas, na abunda ya fada cewa abdullahi dan ubayyi dan salool, yayi magana ta kaskanci garesu, da aka kira jikan salool yayita rantsuwa yana cewa bai fadaba, sai gashi Allah ya karyatashi, ya gaskata ibn Abbas a cikin suratul Munafiqoon.
* cin amana da karya al-kawari
* tarayya da kafurai a bayan fage
* fadin munanan magana ga muslumci da musulmai, kamar fadin Abdullahi dan ubayyi dan salool yayin da suka fita yake yake cewa; "idan muka dawo zuwa madina, masu karfi zasu fitar da masu rauni daga madina", wanda sukace yakeyi ga muhajiruun da manzon Allah.
* Yana daga siffofinsu basa halattar sallar jam'i musamman sallar a suba, idon sunyima sunayi ne don mutane suce su musulmi ne kamar yadda yazo cikin suratun nisa'i [4:142].
* Da sauransu.
*
* Na farko a sama munce munafukin muslumci yana kasancewa ne akarkashin daula ta islama, toshi mu'awuya lokacinda ya muslumta, yana karkashin daula ta kafurci, to wazai munafunta bayan lokacin mafiya yawan musulmai suna madina, kenan karya aka masa.
* Na biyu Mu'awuya ya halarci yakokan manzon Allah SAW bayan Fathu makka, kamarsu Gazwatu Ahzab, Gazwatu hunain, da sauransu, ya kuma riki kwamandan yakuna kafin yayi sarauta, haka kuma lokacin Mulkinsa, yayi yakuna ya bude garuruwa a zamaninsa kamar yadda zamuji nan gaba.
* Na Hudu Babu wani wanda zai kawo maka cewa ma'awuya yana tarayya da kafurai, ko kuma baida rikon amana ko karya Al-Qawali, yana halartar sallah jam'i, baya fadin mummunar magana ga wani kamar yadda zamuji, kyawawan halayensa nan gaba.
*
* Wannan ke nuna karya aka yima sayyidina mu'awuya, domin babbar hujjar Rafidawa, hankali baya daukarta idan mukayi la'akari da wanene munafuki a zamanin Manzon Allah, kai har zuwa yanzu ma. Kawai sunayin hakane don cimma wata manufa tasu maras amfani.
*****
*****
* A Nan zamu tsaya sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu dasa daga inda muka tsaya insha Allah.
**********
*
°

**********
Dan Uwanku; Ibrahim Yunusa Abu-Ammar.
*************************
03/04/1437H - 2016M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter