WANENE SARKIN MUSULMAI MU'AWUYA DAN ABU SUFYAN (R:A) DA YAN SHI'A KE ZAGINSA – fitowa ta daya (1).
************
*
*
1). MENENE SUNAN SA?
*.
* Sunan sa; Mu'awuya dan shakru dan harbu dan umayya dan abdush-shamsi dan Abdul-manafi dan Kusayyi dan kilabu.
*
2). WANENE MAHAIFINSA?
* Mahaifinsa dai shine Abu sufyan, Shakru dan harbu dan umayya dan abdush-shamsi dan Abdul-manafi dan Kilabu daya daga cikin fitattun 'yan majalissar kuraishawa wanda sukaja da manzon Allah SAW kafin Allah ya Azurita zukatansu da karbuwar muslumci Abu sufyan yana daya daga cikin wadanda sukayi kama da manzon Allah SAW.
*
* "Mutane Hudune aka bayyana sunyi kama da manzon Allah SAW a halittar jiki, bayan Al-hasan sai Al-Hussain sannan kuma shi Shakru (Abu Sufyan) mahaifin Sayyidina mu'awuya, sannan da sa'ibu dan ubaidu kakan Imamush-shafi'i.
*
3). WACECE MAHAIFIYAR SA?
* Mahaifiyarsa itace Hindatu Diyar Utbah Dan Rabii'a dan Abdush-shamsi, Ta muslumta da wuri da ita da danta amma basu samu yin Hijira zuwa Madina wajan Manzon Allah SAW ba, saboda rauninsu (Rauni na samun damar tafiya, kasancewar su, ita mata ga dan majalissan kuraishawa shi kuma 'da), Yar uwarsu ramlatu ce tayi hijira itada mijinta, wacce bayan rasuwar mijinta Manzon Allah SAW ya aureta.
*
4). HAIHUWAR SA?
* An haife shi a shekarata goma sha takwas 18 kafin hijira, kenan manzon Allah SAW ya bashi shekara talatin da biyar 35 kenan.
*
5). SIFFAR SA?
* Mu'awuya dogo ne, fari, kyakykyawa mai kwarjini da cikar fuska, Shiyasa ma sayyinina umar ke yi masa laqabi da kisran larabawa (Domin kisra kyakykyawa ne ainun har ana buga misali da kyawunsa a farisa) a lokacin da yake sarauta kuwa ya kasance mai yawan kula da ado da fankama sutura da nufin nuna darajar sarauta da karfin iko.
*****
* A Nan zamu tsaya sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu dasa daga inda muka tsaya insha Allah.
**********
*
•
**********
Dan Uwanku; Ibrahim Yunusa Abu-Ammar.
*************************
02/04/1437H - 2016M
Home
»
Kundun Tarihi
» [Gaskiyar Lamari] WANENE SARKIN MUSULMAI MU'AWUYA DAN ABU SUFYAN (R:A) DA YAN SHI'A KE ZAGINSA – fitowa ta daya (1).