Amfanin Ilimin lissafi, wurin tafiyar da rayuwar Al-umma.- www.zaurensunnah.ga
Assalamu Alaikum, barkan mu da saduwa yan uwa da abokan arziki, ina fatan kuna lafiya kuma fatan kuna cikin farin ciki Allah ya tabbatar mana da Al-khairin sa Amin.
Gabatarwa
Nasan da yawa daga cikin mutane basu san amfani ilimin lissafi ba, a wannan zamani kai dama karnukan da suka gabata, shiyasa da daman dalibai basa mai da hankali ga sanin ko koyan ilimin lissafi, a takaice ma wani ko hanya baya son hadawa da ilimin lissafi balle malamin lissafi.
Domin shi a ganinsa ko tunaninsa ilimin lissafi baya da wani amfani ko fa'ida, a rayuwar al-umma ta yau da kullu, to don me zai bata lokacinsa wurin koyansa, tunda yasan tarawa (+) da debewa (-) da kuma ninkawa (x) da kuma rabawa (/), na yauda da kullu, to mi kuma ya rage masa a ilimin lissafi, da har sai yaje ya koyi wasu shirman da bata lokacine kawai da rashin abun yi.
Abun dai haka yake a wurinka, domin ko shakka babu, ilimin lissafi ilimi ne mai matukar muhimmanci a rayuwar yau da kullu, da kuma harkoki ciki da waje.
- Musamman wannan zamani da ilimin kimiyya da fasaha yayi fice wurin kawo cigaban rayuwar al-umma a zamanan ce, da sawwake ayyukan yau da kullu.
- Yayin da muka mayar da duban mu izuwa ilimin kimiyya da fasaha, zamu lura da cewa kashin bayan ilimin kimiyya da fasaha shine ilimin lissafi, kashin baya ko shine jigo kuma tushe, yayin da ilimin kimiyya da fasaha ya mamaye kaso mai girma na rayuwarmu ta yau da kullum, kama daga bangaren harkokin kasuwancin mu, da ma'aikatun mu, da dai sauransu, da sauran kayan kere-keren da muke amfani dasu, kama daga radiyo, talabijin, na'ura mai kwakwalwa, da sauran masarrafan mu da muke amfani dasu a gida da kuma ma'aikatunmu harma da naurar da nake rubutun nan da ita da wacce kake karatun nan da ita.
- Dukkaninsu kuma kimiyya da fasahace ke samar dasu, shi kuma ilimin kimiyya da fasaha baya tafiya saida ilimin lissafi kamar yadda na ambata a baya, shiyasa zamu ga cewa duk yayin da muke neman shiga wata makaranta kamar makarantun gaba da sakandire, yake zama kusan wajibi ga kowanne dalibi sai yana da shaidar ilimin lissafi kafin ya samu damar shiga makarantar kai tsaye, musamman a bangaren koyon ilimin kimiyya da fasaha, kamar sun likitanci, ilimin na'ura mai kwakwalwa, ilimin kere-kere, ilimin injiniyarin, ilimin gine-gine, da ilimin harkokin kudi, da lissafi (kamar su bank, accounting, fanicial da dai sauransu), da sauran ilimoman harkokinmu na yau da kullu.
- Dukkanin wasu abubuwa da muke amfani dasu a yau, kashi 90 nasu suna karkashin kimiyya da fasaha ne, koda a da basa ciki to yanzu sun nemi matsugunni a wannan inuwar ta kimiyya da fasaha.
- Ilimin kimiyya da fasaha kuma ba bakon abu bane abune dadadde ne kuma sananne, sai dai ban-banci da ake samu daga wannan zamani zuwa wannan zamani sakamakon cigaba, da duniya ke samu a wannan bangaren.
- Yayin da muka koma bangaren harkokin addini kuma zamu ga cewa abune mai matukar muhummanci dake taka muhimmiyar rawa a bangarori da dama, daga cikin su kuwa akwai;
1 - Ilimin rabon gado ilimin wanda al-umma musulma keda bukatuwa zuwa gare shi, domin samun damar taskace dukiyar mamaci, da kuma rabata yadda shari'a ta tanada, yayin da kuma ya kasance bakada lissafi, to raban gado saida ka zama dan kallo amma ilimin sa yayi ta gabanka sai dai waninka, domin sanin +,*,-,/ kaia baya isar maka.
2 - Zakka a bangaren zakka ma haka abun yake, domin kuwa da ilimin lissafine, za'a kididdige dukiyarka, ko ka taskace kayanka don fitar da adadin abunda shari'a ta dora maka da ka fita a kuma lokacinda aka yanka maka, da sauran wasu lissafe-lissafe da suka kebance ta.
- Dama wasu muhimman ayyuka, ko abubuwa da suka shafi addini, wannada ke bukatuwa zuwa ga ilimin lissafi, domin taskacewa ko kididdigewa da rabawa, ko killacewa.
* Haka idan muka juya akalar mu a harkokin mulki ko sarauta, zamu abune sananne kan cewa ilimin lissafi yana da matukar amfani acikin wannan bangaren, idan muka lura zamuga cewa da ilimin lissafine, shugaba zai san wasu adadi na yan kunan sa, ko jama'ar da yake mulka, da muka ma'aikatansa, da wakilansa da sauransu, haka kuma da ilimin lissafine ake kasafin kasa ko jaha, (budget) kenan, wanda a yanzu ma cigaban ya wuce misali, yayin da bajat din ya kasance dukkaninsa yana kammaluwa ne da na'ura mai kwakwalwa (compuer), na'ura mai kwakwalwa kuma masana kimiyyar da fasahar kere-kere ne suka halicceta, yayin da manhajar (software) da ake amfani da ita wajen yin bajat (budget) ma malaman kimiyya da fasahar sadarwa ne suka samar da ita, mai suna 'excel' na kamfanin 'microsoft', da ke cikin kudinsu na 'microsoft office', dukkaninsu kuma kashin bayansu ilimin kimiyya da fasaha ne, shi kuma kashin bayansa ilimin lissafi ne.
Bayan wannan da sauran wasu ayyuka da harkoki masu muhimmanci da mai mulki ko sarauta ke tafiyar dasu a karkashin inuwar ilimin lissafi, kamar biyan ma'aikata albashi da abunda ya kebancesu, kai abunma ya wuce yadda kake zato, domin yanzu haka kaso mai girma na ayyukan gwabnati ana yinsa ne da naura mai kwakwalwa, da kuma online office da sauransu.
* Haka zalika idan muka dubu harkokin ku nayau da kullun, zamuga cewa muna bukatuwa da ilimin lissafine kamar yadda ciki ke bukatar abinci salula kuma take bukatar sim card, kama daga kasuwancin mu, da sauran mu'amalolinmu, kodai muna bukatar ilimin lissafi kai tsaye ko kuma, mu bukaci wani ilimin daban wanda bazai tsayu ba saida ilimin lissafi, wannan kuma wajibi ne, kamar yadda kashi ya zama dole.
.
Idan ko haka ne Ya zame mana wajibi damu dage wurin koyan Ilimin lissafi, wanda yafi ilimin da muke zumudi da shaukin koyo watau ingilishi.
.
Naku MaSoyinku; Abu-Ammar.
16/01/2016M.
Home
»
Kimiyya da Fasaha
» Amfanin Ilimin lissafi, wurin tafiyar da rayuwar Al-umma.- www.zaurensunnah.ga